✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta tura wakili zuwa Majalisar Dinkin Duniya

Taliban na neman damar yi wa shugabannin duniya jawabi.

Gwamnatin Taliban ta kasar Afghanistan ta nada Mohammad Suhail Shaheen, a matsayin Jakadanta a Majalisar Dikin Duniya.

Taliban ta kuma bukaci Majalisar Dinikin Duniya ta ba da damar yin jawabi ga shugabannin duniya a babban taron da ke tafe, ta bakin Mohammad Suhail Shaheen wanda shi ne kakakin Ofisin Siyasar Taliban da ke birnin Doha na kasar Qatar.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric ta ce Taliabn ta aike wa Sakataren Majalisar, Antonio Guterres, wasika a ranar 15 ga Satumba ta hannun sabon wakilin Afghanistan, Ghulam Isaczai, dauke da jerin sunayen wakilan kasar a taron shekera-shekara na MDD karo na 76.

Ta ce, “Kwana biyar da suka wuce Mista Guterres ya samu takarda daga Ma’aiaktar Harkokin Wajen Daular Musulunci ta Afghanistan, dauke da sa hannun Ameer Khan Muttaqi a matsayin  Ministan Harkokin Waje, yana neman amicewar halartar taron.

“Muttaqi ya sanar cewa an hambarar da tsohon Shguaban kasa, Ashraf Ghani a ranar 15 ga Agusta sannan kasashen duniya ba sa daukar sa a matsayin, saboda haka yanzu ba Dujarric ba ne wakilin Afghanistan,” inji ta.

Ta ce shugabannin Taliban na kalubalantar cancatnar wakilin kasar a Majalisar suna kuma sanar da cewa daga yanzu, Mohammad Suhail Shaheen, shi ne mai magana da yawun kasar a Majalisar.

Wani babban jami’i a Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce kasarsa na sane da wasikar amma ba ta da masaniyar yadda kwamitin sulhun Majaliar zai warware tankiyar.

A cewarsa, kwamitin “zai dauki lokaci ya tattauna,” wanda ke nufin da wuya Taliban ta samu damar yin jawabi, musamman a babban zauren taron.

A duk lokacin da aka samu irin wannan takaddamar, kwamiti kan yi zama a kai sannan ya yanke hukunci.

A halin yanzu dai, kwamitin mai mutum tara ya riga ya samu damar fara zama domin yanke hukunci bayan samun sakon daga shugaban zauren MDD Abdulla Shahid.

Mambobin kwamitin su ne kasashen Amurka, Rasha, China, Bahama, Bhutan, Chile, Namibia, Saliyo da kuma Sweden.

A ranar 27 ga watan Satumba, ranar rufe taron, amma har yanzu babu tabbacin wanda zai yi magana da yawun Afghanistan idan har aka amince da Taliban.

A mulkin Taliban na 1996 zuwa 2001, MDD ba ta amince da su ita ba, sai ta ba wa shugabna gwamnatin baya ta Burhanuddin Rabbani kujerar wakiltar kasar, kafin a kashe shi a harin kunar bakin wake a 2011.

A wannan karon kungiyar ta ce tana neman amincewar kasashen duniya da kuma neman taimakon kudade domin gina kasarsu.

Amma kokarin kafa gwamnatin kungiyar na tattare da matsala, kasancewa yawancin ministocin gwamnatin wucin gadin suna cikin jerin mutanen da MDD ta kakaba wa takunkumi bisa zargin ta’addanci ko daukar nauyin ta’addanci.