✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Takarar Shugaban Kasa: Me zai faru idan Buhari bai sa hannu kan Dokar Zabe ba?

A yanzu haka, dokar zabe ta manyan ’yan siyasa ’yan kallo a zaben fitar da ’yan takarar shugaban kasa.

Makomar ’yan siyasa da ke kada kuri’a a matsayin daliget na alfarma saboda suna rike da mukaman siyasa yana tangal-tangal.

A halin da ake ciki, idan Shugaba Muhammadu Buhari bai sa hannu kan Dokar Zabe ta 2022 da ke gabansa ba, daliget na wucin gadi ne kadai za su kada kuri’a a zaben fi da ’yan takarar shugaban kasar jam’iyyun siyasar Najeriya.

Su kuma daliget din alfarma, sai dai su kare a matsayin ’yan kallo saboda a yanzu haka dokar zabe ta kange su daga jefa kuri’a a zaben fitar da ’yan takara.

Jam’iyyar APC mai mulki dai na da deliget na wucin gadi guda uku daga kowacce daga cikin kananan hukumomi 774 da ke fadin Najeriya.

Haka kuma kananan hukumomi shida na Yankin Birnin Tarayya, kowannensu na da daliget na wucin gadi uku da aka zaba.

A halin yanzu dai, jimillar daliget din wucin gadi 2,340 ne za su kada kuri’a a babban taron na APC.

Amma idan Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar zaben kafin ranar zaben fid da dan takarar shugaban kasa na APC da aka shirya gudanarwa ranar Lahadi, deliget din wucin gadi tare da daliget din alfarma ne za su kada kuri’a.

Sanya hannu a kan dokar zaben kafin ranar zaben fitar da ’yan takarar shugaban kasar APC kuma zai sa adadin daliget din da za su jefa kuri’a karuwa zuwa mutum 7, 800.