✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaici ya kashe mahaifiyar daya daga cikin daliban da aka sace a Neja

Mamallakin makarantar ne ya tabbatar da hakan ranar Laraba.

Daya daga cikin iyayen da aka sace daga makarantar Islamiyyah ta Salihu Tanko da ke garin Tegina a Karamar Hukumar Rafi ta jihar Neja ta mutu saboda takaici.

Mamallakin makarantar, Alhaji Abubakar Alhassan ne ya tabbatar da hakan ranar Laraba.

Ya ce tun da farko dai matar ta sume ne bayan samun rahoton cewa dan nata na cikin wadanda aka sace, kafin daga bisani kuma ta ce ga garinku nan, jim kadan da kai ta asibiti.

A cikin wani sakon murya da aka tura wa ’yan jarida, Alhaji Abubakar ya ce adadin daliban da ’yan bindigar suka sace ya kai 150.

“Daya daga cikin iyayen yaran ma ta mutu saboda kaduwa da kuma takaici lokacin da ta sami labarin, nan take aka garzaya da ita asibiti, a inda aka tabbatar da rasuwarta daga bisani,” inji shugaban makarantar.

Ya kuma ce ya tattauna da ’yan bindigar ta wayar salula, inda ya ce daya daga cikin malaman makarantar da aka sace tare da sauran daliban ya fara korafin cewa an fara lakada musu dukan tsiya, har ta kai ga wasu daga cikin yaran ma yanzu ba sa iya tafiya.

Alhaji Abubakar ya ce masu garkuwar sun kuma tuntube shi tare da neman a bayar da Naira miliyan 110 a matsayin kudin fansar daliban.

“Akwai malaman makarantata guda biyu a cikin wadanda aka sace din; mata biyu da namiji daya. Da ’yan bindigar suka tambaye su wa za su kira, sai wadanda suka haddace lambata daga cikinsu suka bayar, ta nan ne suka fara kira na muka fara ciniki.

“Da farko sun bukaci Naira miliyan 300, amma bayan mun fada musu ba mu da ita sai suka rage zuwa Naira miliyan 100.

“A nan ne suka yi barazanar cewa matukar ba mu biya ba a wanann ranar za su kara zuwa miliyan 110, wanda shine adadi na karshen da suka ba mu,” inji Shugaban makarantar.