✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyyar mawaƙi Rarara kan rasuwar Buhari ta bar baya da ƙura

Dubban masoya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari suna ganin Dauda Kahutu Rarara bai kyauta masa.

Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara na ƙara fuskantar matsin lamba daga masoya tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata.

Tun bayan bayyanar labarin rasuwar tsohon shugaban ne, dubban al’umma suka zuba ido suna tsammanin yadda fitaccen mawaƙin zai yi alhinin rasuwar tsohon uban gidansa.

A baya, marigayi Muhammadu Buhari ya kasance mai gida wanda Rarara ke alfahari da shi tare da kare masa muradunsa tun daga farkon hawan mulkinsa a shekarar 2015 har zuwa ƙarshen wa’adin mulkinsa na biyu a shekarar 2023.

Sai dai jim kaɗan bayan Buhari ya sauka daga mulki kuma jam’iyyar APC wacce Rarara ke yi wa waƙe-waƙe ta ci gaba da mulki, sai aka lura tamkar an yi hannun riga tsakanin tsohon shugaban ƙasar da Rarara, inda har mawaƙin ya zargi tsohon shugaban da damalmala ƙasar kafin saukarsa daga mulki.

Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce a wannan lokacin, lamarin da ya kai ga gurfanar da Dauda a gaban kuliya duk da dai daga bisani ƙurar ta lafa kuma mawaƙin ya ci gaba da yi wa sabon shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu waƙe-waƙe na ban mamaki.

A cikin wannan hali ne bayan shekara biyu kacal da saukar tsohon shugaban ƙasar Buhari, Allah Ya karɓi abinsa, kuma a nan ne mutane da dama suka yi dakon jin ta bakin mawaƙi Kahutu.

Sai dai tun bayan bayyanar labarin rasuwar marigayin, Dauda bai ce uffan ba kan har sai bayan kwana uku, inda ya fitar da takaitaccen faifen bidiyo mai ɗauke da muryarsa da kuma yadda ake ƙoƙarin binne gawar mamacin a Daura bayan an kawo ta daga birnin Landan.

A saman wannan faifan bidiyo Dauda ya wallafa a shafin Facebook ya bayyana cewa “Allah Ya jiƙan maza, Allah Ya sa mutuwa hutuce.”

Har wa yau, faifan bidiyon ya buɗe ne da aya ta Alkur’ani, wacce take magana akan cewa dukkan mai rai mammaci ne, daga bisani kuma ya bayyana cewa wannan saƙo ne ga masu baƙin fata kuma a gaya masu yana zuwa.

Sai dai fa binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa wannan saƙo ya bar baya da ƙura domin kuwa, dubban masoya tsohon shugaban ƙasar suna ganin Dauda bai kyauta masa, saboda a cewarsu hatta a saƙon gaisuwar da ya fitar a shafinsa na Facebook bai ambaci sunan Buhari ba.

Kuma wasu suka ce sun yi zargin Dauda Kahutu ya yi wannan waƙar ne ganin cewa ubangidansa Shugaban Ƙasa Tinubu ya tsaya kan lamarin har bayan kammala jana’izar tsohon shugaban.

Wannan dai ya janyo muhawara mai zafi tsakanin masu bibiyar shafin Dauda Kahutu, don kuwa an yi musayar harshe sosai akan lamarin.

Nazifi Salihi Takai cewa ya yi “daga baya ke nan, ya kamata a ce ka ambaci sunan Baba Buhari a addu’arka. Mutumin da a loƙacinsa kuma ta silarsa tauraruwarka ta haska, amma kawai kace “Allah Ya jikan maza!”. Mu dai fatanmu Allah Ya rahamta wa Baba Buhari!”

Shi ma Mus’ab Abdul Maiturare tsokaci ya yi da: “Dauda Kahutu Rarara kai yanzu kana da bakin magana a kan Buhari har ka ce da shi Allah Ya jiƙan maza? Kai fa ka ce Buhari ya yi dumu-dumu da ƙasar nan. Ko ka manta? Kuma ka zo ka kira shi da kalmar maza? Ka ga ke nan abin da ka ce ba haka ba ne a kan shi.”

Ita kuwa Nanerh Hawwerh tsokaci ta yi da cewa “tasa ta ƙare, yanzu shi da mahaliccinsa ne. In tamu tazo Allah Ya sa mu cika da kyau da imani.

Ga bidiyon da mawaƙin ya wallafa: