✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’addanci: Daruruwan mutane sun tsere daga yankin Birnin-Gwari

Motoci sun fi 100 da suka kwashe mutane zuwa wasu wurare daga ranar Asabar zuwa Lahadi a yankin

Daruruwan mutane sun yi kaura bayan ’yan bindiga sun mamaye kauyen Damari da ke Karamar Hukumar Birnin-Gwari ta Jihar Kaduna.

Wata majiya a yankin ta ce motoci sun fi 100 da suka kwashe mutane zuwa wasu wurare daga ranar Asabar zuwa Lahadi a yankin,

“Abin takaici ne ganin yadda mutanenmu suke watsi da gonakinsu da dukiyoyinsu; ’Yan bindiga sun kwace Damari, yanzu haka suna shiga gida-gida su kwashi abinci da dukiyoin jama’a, sai ka ce babu gwamnati,” inji wata wata majiya.

Hakan kuwa ta faru ne bayan ’yan bindiga sun sace sama da mutum 50 a kauyen bayan wani kazamin fada tsakaninsu da ’yan kungiyar Ansaru a makon jiya.

“Mutane ne tserewa da iyalansu saboda babu sojoji; akwai wani fitaccen ma’aikacin lafiya ma da ya sa sojoji suka taimaka wajen kwashe kayan aikinsa daga Damari,” in majiyarmu.

Ta ci gaba da cewa, “Tabbas akwai babban sansanin sojoji a Mu’azu, amma har yanzu ba su kawo dauki ba… watakila wani abin suke jira,” inji majiyar.

Kakagidan Ansaru a Birnin-Gwari

Mazauna yankin dai na ganin gara mayakan na Ansaru da ’yan bindigar da ke garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, suna sace kadarori tare da kashe duk wanda ya yi musu turjiya.

Wani dan yankin ya ce, “A halin yanzu dai ’yan bindiga ke iko suna cin karensu babu babbaka a yankin suna kai wa mutanenmu hari.

Ya ce, “Mutanenmu na ganin ’yan Ansaru a matsayin masu kare su saboda ba sa kai mana hari ballanta fashi.

“Su dai suna kiran mutane zuwa ga akidarsu, musamman matsasa. Sun kuma yi limancin Sallar Idi sannan suna sasanta rikicin fili da na uure da sauransu.”

Amma wani mazaunin yankin ya ce, “Abin tashin hankalin ne yadda mutane suka gwammace ’yan ta’adda da ’yan bindiga.

“Idan ’yan ta’addan na suka gama sauya tunanin mutane, komawa za su yi suna yakar gwamnati da duk wanda ba ya tare da su.”

Fadan Ansaru da ’yan bindiga a Damari

A baya-bayan nan ne ’yan bindiga suka far wa kauyen Damari domin daukar fansa bayan fadan da suka yi da mayakan Ansaru a makon da ya gabata.

A baya, ’yan Ansaru sun yi kaka-gida a yankin da sunan kare mazauna daga ’yan bindiga.

Daga bisani kuma suka tashi daga yankin bayan fadan da ya barke tsakaninsu da ’yan bidniga wanda ya yi sanadiyyar jikkata mutane da dama daga bangarorin biyu.

Wasu majiyoyi sun ce ’yan Ansarun sun koma yankin Danmusa a Jihar Katsina da wani yanki na jihohin Sakkwato da Zamfara.

Wani dan yankin ya ce, “Babu tabbacin ko sun tashi gaba daya ke nan ko zuwa suka yi su karo mutane.”

Yawancin masu kaura daga yankin sun bi ne ta kauyenUnguwar Gajere suka nufi Layin Dan’auta inda hakiminsu ke zaune.

Barnar ’yan bindiga a yankin Birnin-Gwari

Shugaban Kungiyar Masu Kishin Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Usman Fakai, ya ce mutane cike da motoci akalla 20 ne suka fice daga yankin a ranar Juma’a bayan ’yan bindiga sun sace akalla mutum 50.

Ishaq ya ce ’yan bindiga na cin karensu babu babbaka a cikin kwana uku da suka gabata a yankin.

Ya ce, “An kwana biyu ’yan bindiga na aikata ta’addanci a Damari da kauyuka makwabta inda a ranar Alhamis 28 ga Yuli, 2022, suka shiga suna harbi kan mai uwa da wabi.

“Washegari, ranar kasuwa, suka koma suka yi ta kwace babura da kudaden ’yan kasuwa suka kuma sace dabbobi da hatsi wani dan kasuwa,” in ji shi.

Ishaq ya bayyana damuwa kan rashin sojoji a Damari, sannan ya bukaci gwamnati da ta gaggauta tura jami’an tsaro.

Zuwa wannan lokaci dai hukumomin soji da na ’yan sanda da ma Gwamnatin Jihar Kaduna ba su ce komai game da wannan lamari ba.

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Hamza Idris (Abuja) & Mohammed I. Yaba (Kaduna).