✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

T.Y. danjuma ya yaba da jajircewar daliban yankin Arewa Maso Gabas

Shugaban Kwamitin Sake Farfado da Yankin Arewa Maso Gabas Laftana-Janar T.Y. danjuma GCON (mai ritaya) ya yaba da irin jajircewar da daliban da ke yankin…

Shugaban Kwamitin Sake Farfado da Yankin Arewa Maso Gabas Laftana-Janar T.Y. danjuma GCON (mai ritaya) ya yaba da irin jajircewar da daliban da ke yankin Arewa maso Gabas suka yi wajen ci gaba da yin karatu a sababbin makarantun da suka tsinci kansu a ciki saboda tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yankunan su.

Janar T.Y. danjuma ya yi wannan yabon ne a lokacin da Alhaji Tijjani M. Tumsah ya wakilce shi a ziyarar da kwamitin ya kai Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Zariya (FGGC) inda ya gana da daliban da ke karatu a matakin SS1 da ma’aikata da kuma mahukunta Kwalejin.

daliban suna daga cikin dalibai dubu 2 da aka yi wa canjin makaranta zuwa wasu sassa da ke kasar nan ciki har da Zariya a shirin da kwamitin na aikawa da daliban zuwa makarantun da ba su da hadari a sassan kasar nan (Safe School Initiatibe).

A kan kawo irin wadannan dalibai ne daga Jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe musamman wadanda aka kona makarantunsu ko aka lalata a lokacin yakin Boko Haram don su ci gaba da yin karatu.

A yayin ganawa da daliban Alhaji Tumsah ya hore su ne da su ci gaba da jajircewa da kuma nuna kwazo wajen yin karatu.  “Za mu ci gaba da sanya ido a harkar karatunku don ganin kun zama ’yan kasa nagari ga iyalanku da kuma sauran al’umma baki daya”, inji shi.

A nata jawabin, Shugabar Kwalejin Dokta Asma’u Y. Abdulkadir ta yaba da yadda daliban suka mayar da hankali wajen yin karatu tun bayan da aka mayar da su kwalejin.

Ziyarar dai wata hanya ce da kwamitin yake bi wajen tantance irin halin da daliban da akan tura irin wadannan makarantu suke ciki tun bayan da aka fara aiwatar da shirin a watan Yulin 2017.  Sannan wata hanya ce kwamitin ke gano irin matsalolin da daliban ke fuskanta da kuma hanyoyoyin da za a bi don magance su.

Daga cikin irin wadannan makarantu da kwamitin ya kai wa ziyara sun hada da Kwalejin ’Yan Mata Ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) da ke Bauchi da wacce take garin Azare dukkaninsu da ke yankin Arewa maso Gabas.  Sauran makarantun sun hada da Kwalejin ’Yan Mata Ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) da ke Bida, da Kwalejin Gwamnati (FGC) da ke Minna da wacce ke Ilori da kuma Kwalejin FSTC da ke Kuta-Shiroro da Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Abaji dukkaninsu da ke yankin Arewa ta Tsakiya.  Sauran makarantun sun hada da Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Zaria da takwararta da ke Kano da wacce ke Kaduna da Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) da ke Gusau da Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Sakkwato da kuma Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) da ke Tambuwal dukkaninsu da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

A yayin ziyarar kwamitin kan gana ne da dalibai da ma’aikata da kuma hukumomin makarantun don a tattauna batutuwan da suka shafe su don a nemi hanyoyin da za a bi wajen ganin an warware su.

Idan za a tuna, yakin Boko Haram dai ya yi sanadiyyar lalata makarantu kimanin 1,100 a yankin Arewa Maso Gabas yayin da aka yi asarar malamai kimanin 600.  Kimanin makarantu 43 ne kwamitin ya ware wajen tura daliban SS1 ci gaba da karatu a cikinsu a bangarori daban-daban na sassan kasar nan.