✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Turkiyya sun kashe shugaban IS Al-Qurashi

Sojin leken asirin na Turkiyya sun jima suna farautar Al-Qurashi.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce sojojin leken asiri na Turkiyya sun gano tare da kashe shugaban IS, Abu Hussein Al-Qurashi.

A wata hira da kafar yada labaru mallakar gwamnatin Turkiyya, Shugaba Erdogan ya ce an kashe Al-Qurashi ne a Syria ranar Asabar.

A cewarsa, wannan nasara da aka samu na zuwa ne bayan sojojin leken asirin na Turkiyya sun jima suna farautar sa.

Rahotanni sun ambato majiyoyin tsaro na Syria na cewa sojojin Turkiyya sun kai samame a garin Jandaris da ke Arewacin kasar a daren Asabar inda aka rika jin karar fashewar abubuwa.

Bayan wannan bayanin dai Erdogan bai yi karin haske kan kisan ba, sannan babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da mutuwar Al-Qurashi.