✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sojojin Chadi na sayar da makamansu in suka shiga matsalar kudi’

Sojojin na Najeriya sun zargi sojojin Chadi da sayar da makamai in suka shiga matsi.

Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ta zargi sojojin kasar Chadi da sayar da makamansu ba bisa ka’ida ba.

Kwamando Jemila Abubakar ce ta yi zargin, lokacin da ta wakilci Babban Hafsan Ruwan Najeriya, Awwal Gambo, a wani taron jin ra’ayin jama’a da kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilan Najeriya ya shirya ranar Litinin a Abuja.

An dai shirya taron ne da nufin jin ra’ayin jama’a a kan wasu kudurori guda hudu da Majalisar ke kokarin amincewa da su kafin su zama doka.

Yayin da take tsokaci a kan kwararowar kananan makamai, Jemila ta ce makaman da manyan kasashe ke bayar da su tallafi ga makwabtan kasashe na fada wa hannuwan da basu dace ba.

Ta ce, “Ina daga cikin wadanda ke sahun gaba wajen yaki da Boko Haram, kuma zan iya bugun kirji in tabbatar muku da cewa wasu daga cikin kasashe makwabtanmu basu da makamai.

“Sam ba su da makamai. Yawancin makamansu tallafi ake basu daga…ba na son na ambaci suna…kasashen da suka ci gaba, a kokarinsu na tallafa mana suna kara ta’azzara matsalar tsaron Najeriya.

“Alal misali, za ka ga kusan duk sojan kasar Chadi yana da tsakanin makami 20 zuwa 30 a karkashin gadonsa. Idan ya shiga matsalar kudi, sai ya fito da su ya sayar tsakanin Dala 30 ko Dala 20. Ni nake fadin wannan gaba gadi, in akwai mai musu, ina kalubalantarsa.

“Tun da dai za mu hada gwiwa da sauran kasashen Afirka ta Yamma da sauran kasashen da suke bayar da tallafin irin wadannan makaman, ina tunanin ya kamata mu tsaya kai da fata cewa ko dai su kirkiri dokokin da za su hana yaduwar makamai sakaka a wadannan kasashen ko kuma ba mu ba zaman lafiya,” inji ta.

Ya zuwa yanzu dai sojojin kasar ta Chadi ba su mayar da martani ba a kan zargin.

A lokuta da dama a baya dai, Najeriya ta sha neman taimakon kasar ta Chadi wajen yaki da ta’addanci.