✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ragargaji ’yan ta’adda a Binuwai

Dakarun rundunar Soji ta OPWS, sun bindige ’yan ta’adda a wata musayar wuta da suka yi ranar Lahadi da dare a yankin Adaka na Karamar…

Dakarun rundunar Soji ta OPWS, sun bindige ’yan taadda a wata musayar wuta da suka yi ranar Lahadi da dare a yankin Adaka na Karamar Hukumar Makurdi, Jihar Binuwai.

Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa, shigar ’yan bindigar yankin na Adaka don yin fashi ke da wuya sai sojojin suka kawo wa wurin dauki.

Majiyarmu ta ce mazauna kauyen ne suka sanar da sojojin yayin da suka ga gilmawar motarsu ta sintiri don su kawo musu dauki daga harin yan ta’addar.

Sun ce maharan na shiga garin da misalin karfe 8:00 na yamma suka bindige wata mata da mijinta.

Kwamandan rundunar OPWS, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya tabbatar cewa jami’ansu sun yi arangama da ’yan ta’addar a yankin na Adaka.

“Rundunarmu a shirye kuma a ankare take da yanayin tsaro, don haka za mu yi iya iyawarmu tare da hadin guiwar ragowar jami’an tsaro wurin kare lafiyar jama’a”,  inji shi

Yekini, ya ce sashen yada labarai na shalkwatarsu a shirye yake a wurin karbar bayanai a kowane lokaci masu alaka da irin wannan.