✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ragargaji Boko Haram a Geidam

Mayakan Boko Haram sun kai hari a yayin da ake shagalin Babbar Sallah.

Sojojin Najeriya sun murkushe harin mayakan kungiyar Boko Haram a yayin da ake bukukuwan Babbar Sallah a garin Geidam na Jihar Yobe.

Maharan sun gamu da luguden wutar sojojin ne a lokacin da suka yi yunkurin kutsawa zuwa cikin garin da tsakar dare.

Wani mazaunin Geidam, Modu Ali ya ce mazauna garin sun shiga cikin tashin hankali, amma maharan “Ba su yi nasara ba a wannan lokacin saboda sojoji sun yi saurin hana su shigogwa saboda mutanen gari sun kai musu rahoto”.

An kai harin ne bayan wasu daga cikin dubban mutanen garin sun koma domin yin bukukuwan Babbar Sallah bayan sun yi gudun hijira kimanin wata biyu da suka wuce lokacin hari da kuma mamayar da kungiyar ISWAP ta yi wa garin.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya jinjina wa jami’an tsaron da suka ragargaji mayakan kungiyar.

Sanarwar da kakakin gwamnan, Mamman Mohammed, ya fitar ta ce, “Duk da cewa maharan sun janye, sojoji sun bi su sun murkushe wani harin kwanton baunar da suka nemi kaiwa.

“Gwamnati da jama’ar Jihar Yobe sun yaba da jarumtar sojojin wajen samar da aminci domin ganin mutane sun yi bukukuwan Babbar Sallah cikin aminci”.

Ya ce saurin daukar mataki zai magance hare-haren Boko Haram, don haka ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da kai wa jami’an tsaro rahoton duk take-taken da ba su gamsu da shi ba a kan lokaci.