✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 78 a dazukan Zamfara

Hare-haren dai sun yi sanadiyyar kashe 78 daga cikinsu.

Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin ’yan bindiga da dama bayan wasu jerin hare-hare da suka kai da jiragen yaki a dazukan Jihar Zamfara.

Hare-haren jiragen yakin sun kuma yi sanadiyyar kashe ’yan bindigar akalla 78, kamar yadda wata majiya daga cikin sojojin ta shaida wa kafar yada labarai ta PRNigeria ranar Juma’a.

A cewar majiyar, “Sashen sojojin sama na rundunar tsaro ta Operation Hadarin Daju ta kai wasu jerin hare-hare kan ’yan bindiga a Jihohin Arewa maso Yamma a cikin kwana uku.

“A kokarinta na kakkabe yankin daga ayyukan ’yan bindiga, rundunar ta mayar da hankali a kan yankunan da aka fi samun taruwarsu, musamman a dazukan Dansadau da Kuyambana a Jihar Zamfara.

“A sakamakon haka, a ranar biyu ga watan Agustan 2021, rundunar sojojin Najeriya ta gudanar da shawagin leken asiri kan wadannan wuraren a kan ’yan bindigar da ke yawo a babura a dazukan kauyukan Dansadau da Kuyambana.

“Mun sami nasarar bibiyarsu tare da gano sansanoninsu da dakunan da suka giggina a ciki.

“Bayan ta yi amfani da jiragen yaki masu kirar ‘MI 171’ da kuma ‘Agusta 109’, rundunar ta ragargajesu da yammacin biyu ga watan Agustan 2021 tare da hadin gwiwar dakarun sojin kasa wadanda su kuma suka yi musu kofar rago ta kasa

“Hakan dai ya jawo kashe 78 daga cikinsu, wanda ala tilas suka gudu suka hakura da sansanin,” inji majiyar.

Kazalika, sojojin da suka yi aiki ta kasa yayin hare-haren sun tabbatar da kakkabe ragowar ’yan bindigar da ke raye daga dajin.