✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 50 a Zamfara

Bayan gwabzawa, sojoji sun kwato shanu 334 daga hannun 'yan bindigar.

Rundunar Sojin ‘Operation Hadarin Daji’ a ranar Asabar ta yi nasarar kashe ‘yan bindiga sama da 50 a kauyen Kuriya da ke Karamar Hukumar Kauran-Namoda a Zamfara.

Jami’in Watsa Labaran Hedikwatar Tsaro Manjo-Janar John Enenche ne ya bayyana haka a ranar Lahadi.

Enenche ya ce bayan kashe ‘yan bindigar yayin arangamar da suka yi, sojojin sun kwato shanu 334.

Ya kara da cewa, an kai harin ne da taimakon Rundunar Sojin Sama ta Najeriya.

Ya ce sun kai harin ne bayan samun rahoton ayyukan ‘yan bindiga a kauyen.

Sai dai ya ce sojoji hudu sun ji rauni, yayin gwabzawar da aka yi da ‘yan bindigar.

Ya kuma yin bayani cewa a Jihar Katsina kuma, sojoji sun kwato shanu 62 a kauyen Dunya da ke Karamar Hukumar Danmusa a Katsina.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun tsere sun bar shanun don kar sojoji su riske su.

A yanzu jami’an tsaro sun mamaye yankin da ‘yan bindigar suka fi kai farmaki, domin dakile ayyukan ta’addanci.

Hedikwatar Tsaron ta jinjina wa dakarun bisa nasarar da suka yi, sannan ta ba su kwarin gwiwar ci gaba da kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga da suka addabi wasu yankuna na kasar nan.