✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji Sun Kashe Kwamandojin ISWAP 2 A Borno

Soji da Civilian JTF sun kashe kwamandoji da mayakan ISWAP a yankin karamar hukumar Konduga ta Jihar Borno.

Dakarun sojin Najeriya tare da mayakan sa-kai na  Civilian JTF  sun kashe kwamandojin kungiyar ISWAP guda biyu a yankin Yuwe na karamar hukumar Konduga ta Jihar Borno.

Kwamandojin da sojoji suka kashe a musayar wuta dai su ne Abu Huzaifa da wani Sarki da ya jagoranci kungiyar ISWAP a Dajin Sambisa kusan shekaru goma.

Wata kwakkwarar majiya ta bayyana cewa sojojin da ke aikin hadin gwiwa sun kuma “kashe ’yan ta’adda da dama yayin da wasu suka tsere raunukan harbin bindiga,”  a artabun na ranar Asabar, 6 ga Mayu, 2023.

Ta ce, “Kwamanda ISWAP din da dakarun suka kashe, wato Sarki, ya jagorancin kai hare-hare da dama a Bita da Mubi da Adamawa da Madagali.

“Akwai  karin wasu kamar su Abou Huzaifa, Abou Ubaida da  Abba Tukur, wadanda su ma aka kashe.”

Majiyar ta kara da cewa, “Sojojin sun rasa daya daga cikin ’yan Civilian JTF, amma sun kwato alburusai da babura da kekuna takwas da kuma kayayyakin masarufi a wannan arangamar.”