✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Monguno

An shafe tsawon minti 30 ana dauki ba dadi da mayakan na Boko Haram.

Dakarun hadin gwiwar soji sun dakile wani harin kungiyar Boko Haram a garin Monguno da ke Arewacin Jihar Borno.

Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama, wani masani kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa ’yan ta’addan sun kutsa cikin garin da muggan makamai da misalin karfe 12:30 na daren ranar Lahadi.

Majiyar ta ce ’yan banga da ke karkashin rundunar MNJTF sun fafata da su a wani kazamin artabu da aka kwashe kusan mintuna 30 ana yi, inda suka yi nasarar fatattakar maharan.

Ba a dai fayyace adadin wadanda suka jikkata ko suka mutu daga bangarorin biyu ba.

Monguno na daga cikin kananan hukumomi 27 na Jihar Borno kuma tana da tazarar kilomita 137.8 da Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

A baya dai garin ya sha fama da munanan hare-hare daga kungiyar ta’addanci.