✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun bindige kasurgumin dan ta’addan Binuwai

Rahotanni daga Jihar Binuwai na cewa an bindige kasurgumin dan tayar da kayar baya da ake nema ruwa a jallo a Jihar, Terwase Akwasa, wanda…

Rahotanni daga Jihar Binuwai na cewa an bindige kasurgumin dan tayar da kayar baya da ake nema ruwa a jallo a Jihar, Terwase Akwasa, wanda aka fi sani da ‘Gana’.

A ranar Talata sojoji suka cafke Gana a daura da shataletalen Yandeve, da ke Karamar Hukumar Gboko da Jihar.

Majiyarmu ta ce an kashe mutumin da ake nema ruwa a jallon ne jim kadan bayan sojojin sun yi awon gaba da shi.

Majiyar ta aike wa wakilinmu hoton gawar da ta ce ta Terwase ce an yi mata ruwan harsasai ba tare da yin karin bayani ba.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, wakilinmu bai kai ga samun tabbaci game da abin da ya faru ba.

– Yadda aka cafke Gana –

Sojojin sun damke Gana tare da wasu yaransa ne a yayin da Majalisar Masarautar Sankera daga Karamar Hukumar Katsina-Ala ta Jihar ke kokarin kai ’yan dabar garin Makurdi domin a yi musu afuwa.

A ranar Talatar da dare, Gwamna Samuel Ortom ya ce sojoji sun tsare Gana da yawancin yaransa ne a hanyar kai 172 daga cikin ’yan ta’addar da suka amince su ajiye makamai domin a gabatar da su ga Majalisar Tsaron Jihar.

“Gana na cikinsu kuma an kama shi tare da wasu da dama aka yi awon gaba da su a cikin motarsu [sojojin].

“Mun yi magana da Janar Yekini wanda ya tabbatar mana cewa su ne suka yi kuma za su kawo su daga baya”, inji shi.

Daga baya Ortom ya ce wasu daga cikin yaran sun koma Katsina-Ala, wasu 42 kuma sun isa Gidan Gwamnatin Jihar da ke Makurdi.

– Shekara hudu yana buya

Da farko a ranar Talatar, Gana ya shammaci jama’a a filin wasa na Akume Atongo da ke Katsina.

Karon farko ke nan da ya bayyana bayan shekara hudu yana buya, da nufin samun sabuwar afuwar gwamantin jihar a karo na biyu.

– Sabon shirin yafiya –

Gwamnatin Jihar Binuwai ta bullo da sabon shirin afuwar ne bayan taron dattawa masu ruwa da tsaki na Sankera mako biyu da suka gabata.

A lokacin zaman ne Gana da yaransa suka amince su ajiye makamansu a yi musu afuwa.

Sakakamon haka manyan yankin da suka hada da ’yan siyasa suka matsa wa Gwamna Ortom lamba cewa ya sasanta da ’yan gungun da ake nema ruwa a jallo.