✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojin ruwan Najeriya sun kama jirgin Norway da satar danyen mai

Jirgin ya tsinke a guje ya nufi iyakar Najeriya da Sao Tome and Principe a kokarinsa na tserewa.

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta yi nasarar kame wani jirgin ruwa kasar Norway yana kokarin satar danyen mai a yankin Akpo mai arzikin mai da ke birnin Fatakwal a Jihar Ribas

Jaridar Premium Times ta ruwaito babban jami’in rundunar sojin ruwa mai kula da manufofi da tsare-tsare, Rear Admiral Sa’idu Garba yana fadin yayin ganawa da manema labarai ranar Juma’ar nan a Abuja.

Bayanai sun ce, jirgin mai suna MT HEROIC IDUN, ya shigo iyakar Najeriya ta ruwa, ya kuma nufi rijiyar mai ta Akpo inda ake hakar danyen mai, a ranar 7 ga watan Agusta da tsakar dare, ba tare da izinin Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) ba.

A cewar Rear Admiral Sa’idu Garba, bakon jirgin ruwan ya shigo ne da niyyar dibar danyen mai a rajiyar man ba tare da izini ba, wanda aka yi sa’a rundunarsu ta dakatar da shi.

“Sakamakon binciken mu ya nuna cewa jirgin ba shi da izinin hukumar da ta ke da alhakkin ba jirgin izini zuwa rijiyar da ake hakar man, watau NNPC” in ji shi.

Wannan a cewarsa, shi ya wajabta wa rundunar wani jirgin ruwanta mai suna NNS GONGOLA ya yi binciken kwakwaf kan bakon jirgin dako man a ranar 8 ga watan Agusta.

Sai dai bakon jirgin ya ki bin umarni rundunar jirgin na NNS GONGOLA, inda ya tsinke a guje ya nufi iyakar Najeriya da Sao Tome and Principe a kokarinsa na tserewa.

Baya ga kokarin tserewa, matukin jirgin ya rika fitar da sanarwar karya ga mahukuntan kasa-da-kasa da cewa, ya yi zargin jirgin NNS GONGOLA na ‘yan fashin teku ne wanda hakan ta sa ya tsere don batar da sawu.