A iya cewa zuwa yanzu an kawo karshen babban zaben bana, in ban da zaben gwamnonin jihohin Adamawa da Ribas tare da na ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas. Yayin da aka sake gudanar da zaben raba-gardama na Gwamnan Jihar Adamawa a jiya Alhamis, bayan da Alkalin Babban Kotun Jihar Mai shari`a Abdul’azeez Waziri ya janye umurnin kotunsa na hana yin zaben da farko, sakamakon karar da dan takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyyar MRDD, Rabaran Eric Theman ya shigar yana kalubalantar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a kan kin sa dagin jam’iyyarsa da hukumar ba ta yi ba.
An dai gudanar da zaben raba-gardamar ne a Jihar Adamawa a tsakanin Gwamna mai ci na Jam’iyyar APC Alhaji Muhammadu Jibrilla Bindow da dan takarar Gwamnan Jihar na Jam’iyyar PDP, Alhaji Ahmadu Umar Fintiri, wanda a zaben ranar 9 ga wannan wata shi ke kan gaba da kuri’a dubu 367 da 471, yayin da Gwamna Bindow ke bi masa da kuri’a dubu 334 da 995, wato akwai ratar kuri’a dubu 32 da 476, alhali akwai kuri’a dubu 40 da 988 a mazabu 44, da aka soke kuri’unsu bisa ga wasu dalilai. Mai yiwuwa mai karatu lokacin da kake karata wannan makala sakamakon zaben raba-gardamar Adamawa ya fito.
A can Jihar Ribas kuwa Hukumar INEC ta tsayar da ranar Asabar 13, ga Afrilu don gudanar da zaben Gwamna da ’yan Majalisar Dokokin Jihar ne da hukumar ta kasa gudanarwa a ranar 9 ga Maris da aka yi zaben gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi, saboda irin balihirar da ta rika barkewa a kusan dukan sassan jihar. Daga sakamakon zabubbukan da Hukumar INEC ta gudanar a bana, dan takarar Jam’iyyar APC kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben da kuri’a miliyan15 da dubu 191 da 847, yayin da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya zo na biyu da kuri’a miliyan 11 da dubu 262 da 978. Jamiyyar ta APC ita take da ’yan Majalisar Dattawa mafi rinjaye har 65, PDP na da 43, sabuwar Jam’iyyar YPP na da 1, a majalisar mai wakilai 109.
A Majalisar Wakilai mai wakilai 360, daga sakamakon zaben da aka bayyana zuwa yanzu, Jam’iyyar APC tana da wakilai 223, yayin da PDP take da 111, sauran jam’iyyu suna da wakilai 14, sauran wakilai 12 da suka rage ana dakon sakamakonsu. Daga sakamakon zaben gwamnonin jihohi kuwa zuwa yanzu Jam’iyyar APC na da gwamnonin jihohi 20, yayin da Jam’iyyar PDP ke da gwmnonin jihohi 13, sai Jam’iyyar APGA mai Gwamna 1. Saura sakamakon gwamnonin jihohin Adamawa da Ribas, sai abin da sakamakon zabubbukansu ya tabbatar in an gudanar da su. A zabubbukan na bana ba a yi zaben gwamnoni a jihohin Edo da Ondo da Bayelsa da Kogi da Ekiti da Anambra ba, saboda su a lokuta daban-daban ake yin su bisa ga hukunce-hukuncen kotunan zabe a kansu a baya.
A ganina tsarin siyasar da aka yi bana a Jihar Kano ita ta fi daukar mini hankali, bisa ga irin yadda ta kama hanyar zama siyasar birni da kauye, siyasar da Kano ba ta gada ba. Alal misali a Jamhuriya ta Daya Jam’iyyar NPC ta marigayi Sardaunan Sakkwato kuma Firmiyan Jihar Arewa, Sa Ahmadu Bello da ta kara da Jam’iyyar NEPU SAWABA ta marigayi Malam Aminu Kano a nan Arewa, tushenta kuma Kano, da rana daya ba ta taba bayyana da batun dan birni da dan kauye ba. Haka a Jamhuriyya ta Biyu a 1979 zuwa 1983, Jam’iyyar PRP da ta zama gyauron NEPU, ba ta gudanar da siyasarta a Kano da sunan dan birni da dan kauye ba. Domin da a nuna wannan bambanci ta yi tafiya da ba ta tsayar da marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi dan takarar Gwamnan Jihar ba, bayan soke Injiniya Salihi Iliyasu dan cikin tsakiyar birnin Kano.
Haka labarin rashin nuna wannan bambanci na dan birni da dan kauye ya ci gaba da tasiri a cikin siyasar jihar ta Kano akan mutane irin su Sanata Kabiru Gaya da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da zabebben Sanata Malam Ibrahim Shekarau da shi kansa Gwamna mai ci, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a lokuta daban daban da suka shiga siyasa suka kuma yi nasarar lashe zaben zama Gwamnan Jihar Kano. Wanda da wancan batu na siyasar dan birni da dan kauye ya yi tasiri, to, kuwa kila da yawansu da ba su zama Gwamna a jihar ba.
Amma a zaben bana da Gwamna Ganduje ya fafata da Injiniya Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar PDP, Abban da ya fito daga Unguwar Gwale ta Karamar Hukuma Gwale da ke tsakiyar birnin Kano, sakamakon zaben farko da na raba-gardamar, duk sun tabbatar da cewa masu zabe sun rarrabu ne a kan ’yan birni da ’yan kauye. Alal misali daga cikin kananan hukumomi 28, da aka sake zaben, biyu ne kawai na cikin birni da kewaye wato Nasarawa da Dala, nan ne kadai Injiniya Abba Kabir ya tabuka wani abu, amma a sauran kananan hukumomi 26, bai yi wata rawar gani ba, kai karewa da karau a kananan hukumomi irin su Makoda, Abba bai samu ko kuri’a daya ba, sabanin Ganduje da ya samu 360. A Karamar Hukumar Garun Malam ma Abba kuri’a daya tilo ya samu yayin da Ganduje ya samu kuri’a 235.
Mai karatu ba za ka gane batun da nake yi ba, har sai ka bi sawun yadda sakamakon zaben wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa da na jiha suka kasance, inda a zaben ’yan Majalisar Dattawa duka uku na jihar da na ta wakilai 24, da na Shugaban Kasa ’yan takarar Jam’iyyar APC suka yi nasarar lashe shi, Jam’iyyar PDP ko kujera daya ba ta samu ba, alhali kafin zaben kusan raba daidai ake tsakanin APC da PDP, musamman a majalisun dokoki na kasa. A zaben Majalisar Dokokin Jihar mai wakilai 40, PDP ta samu 12, wadanda ak asarinsu daga mazabun birnin Kano da kewaye ne, ita kuma APC ta samu 28, da suka fito daga karkarar jihar. Ya kamata mai karatu ya fahimci cewa, mutane biyu da suke jagorancin siyasar Kano a yau wato Gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso duk ’yan karkara ne, amma a zaben Gwamna sai ta koma batun Abba da Ganduje, wato dan birni da dan kauye. Muddin kuma wannan tsarin siyasar birni da kauye da aka dade ana yin sa a wasu jihohi ya samu gindin zama a tsarin siyasar Jihar Kano, to, kuwa siyasar Kano za ta samu koma-baya a kan yadda aka san ta na siyasar ra’ayi da neman CANJI.