✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sinadarin soyayya: Kashi na biyu

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Za mu ci gaba da bayaninmu kan ilimin soyayya domin ma’aurata su fahimci wannan babban jigo na rayuwar aure kuma su dabbaka da alkinta soyayyar cikin huldodinsu da zamantakewar aurensu:

A kashin da ya gabata mun faro bayani kan sinadaran soyayyar auratayya inda muka ambaci abu na farko daga cikin sinadaren soyayyar auratayya, wato shakuwa da abubuwan da ya kunsa a karkashinsa.

Yau kuma za mu daura daga abu na biyu wato Sha’awa sannan mu ci gaba.

 

2. Sha’awa:

Wannan shi ne sinadari na biyu cikin Sinadaran Soyayyar Auratayya.

A dangantaka ta tsakanin ma’aurata, komai karfin shakuwarsu, idan ya kasance ba cikakkiya kuma daidaitacciyar sha’awa a tsakaninsu, to shakuwar nan za su ji ta salaf ne, domin sha’awa ita ce gishirin rayuwar aure.

Kamar yadda shakuwa ke rike aure ya yi tsawon rai da inganci, to haka ma sha’awa ke iya rike aure ya yi tsawon rai ko da ba inganci sosai a cikinsa.

Domin akwai ma’auratan da babu shakuwa da fahimtar juna tsakaninsu, kullum suna cikin jayayya da juna amma sai aurensu ya dade saboda kasancewar daidaitacciya kuma cikakkiyar sha’awa a tsakaninsu.

Matsalar sha’awa tsakanin ma’aurata na daya daga cikin ’yan gaba-gaban abubuwan da ke saurin kawo mutuwar aure musamman idan ya kasance mijin bai samun yadda yake so daga wajen matar saboda yanayin karfin bukatuwar sha’awar da namiji.

Mafi yawan mata kuwa na tsananin hakurin jure wa matsalar sha’awa da suke fuskanta daga mazansu.

Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (5)

 

Fuskokin Sha’awa Cikin Rayuwar Aure

  1. Wadansu ma’auratan tun farkon haduwarsu sun kasance suna tsananin sha’awar junansu, kila ma sha’awarce ta yi dalilin kulluwar soyayyarsu.

Irin wannan sha’awa takan kasance mai karfi kuma mai wuta-wuta, sannan ma’auratan na yawan jin maganadisunta na gittawa tsakaninsu.

Don haka abu kadan zai sa su ji suna son kasancewa da juna.

Wannan shi ke sa su rika kwakwar juna su ji ba su son rabuwa da juna.

Sai dai irin wannan sha’awa ba ta tsawon rai cikin rayuwar aure, nan da nan take mutuwa murus a neme ta a rasa musamman idan wasu abubuwa suka shigo cikin rayuwar aure wadanda da can babu su.

Abin da kadai zai iya hana irin wannan sha’awa mutuwa murus shi ne idan ya kasance lokacin da suke cikin magagin sha’awar, ma’aurata sun yi kokari sun kulla aminci tsakaninsu; sun yi kokari sun bude hanyar sadarwar da za ta kai su ga samun fahimtar juna.

Haka kuma sun yi kokari sun shiga ran juna ta hanyar kyautatawa da kokarin faranta wa juna rai, wanda zai sa su shaku sosai.

To a irin haka ko wutar sha’awarsu ta mutu, ba za ta mutu murus ba, kuma akwai yiwuwar ta sake ruruwa nan gaba.

Amma idan babu irin haka, to idan ta mutu ta mutu ke nan har abada.

 

  1. Sai kuma yanayin sha’awar da ke girma da nuna tare, girma da nunar dangantakar da ke tsakanin ma’aurata; wato ma’aurata na kara shakuwa, sha’awar da ke tsakaninsu na kara tsima da dumama.
  2. To irin wannan haka za su girma su tsufa da sha’awarsu sai dai idan wani gawurtaccen abu ya fado cikin rayuwar aurensu wanda ya girmama har ya iya ruguza gaba daya soyayyar da ke tsakaninsu.

To wannan na iya sa su duka ko wani bangare daga cikinsu ya ji ya daina sha’awar dayan kamar yadda takan faru ga wadansu matan yayin da mazansu suka kara aure.

 

  1. Wadansu kuma ma’auratan sukan samu bambancin sha’awa tun farkon aurensu, misali: Yakan kasance maigida yana da sha’awa mai karfi kuma mai yawa, ita matar tana da ’yar kadan.

A irin haka idan ya kasance matar ba ta fuskantar wata matsala a cikin wannan aure sai wannan kadai, to yawanci sukan yi hakuri su daure, amma duk da haka abin na damunsu.

Ko maigida yana tsananin sha’awar matarsa yana kwakwar kasancewa da ita, ita kuwa kwata-kwata ba ta sha’awar mijin kuma tana bari ya kusance ta ne kadai a kan dole; ba wai domin ba ta da sha’awa ba, kawai shi din ne ba ta sha’awa.

Yawanci irin haka ya fi faruwa ga matan da aka yi wa auren dole kuma ya kasance ko bayan auren sun ci gaba da tsanar mazan da suke aure, to a irin haka mawuyacin abu ne su ji suna sha’awar mazan nasu.

Yana iya kasancewa maigida sha’awarsa ’yar kadan ce kuma marar karfi, ita kuma matar ya kasance tana da sha’awa mai yawa.

A irin haka yawanci mata suna hakuri su zauna idan auren ya kasance bai da wata matsala sai wannan kadai.

Ko ya kasance uwargida na tsananin sha’awar da kwakwar maigidanta, amma shi sai ya ji ba ta burge shi ta fannin sha’warsa.

To a irin haka idan ba an samu miji mai zurfin tunani da hangen nesa ba, nan da nan zai rabu da ita.

Sai mako na gaba insha Allah da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.

 

Nabeela Ibrahim Khaleel

[email protected]

08063675635