Assalamu alaikum; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen labarin Farfesa Khalid Al Jubair da kuma ci gaban misalan da’a ga Allah daga daidaikun mata na wannan zamanin da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.
Farfesan ya cikashe labarinsa da cewa: “Bayan shekara daya da rabi da sallamarsu, aka sanar da ni wani mutum da matarsa suna son ganina. Na je na same su sai na ga iyayen yaron da na yi wa aiki ne. Yanzu shekarunsa 5. Yana cike da koshin lafiya kamar sabon fure. Tare da su kuma jariri ne dan wata hudu. Na yi maraba da su cikin karamci, cikin wasa nake tambayar mahaifin yaron jaririn na 13 ko 14 cikin ’ya’yansa? Ya kalle ni cike da murmushin al’ajabi kamar yana tausaya mini. Sannan ya ce wannan shi ne na biyu wanda ka yi wa aiki kuma shi ne na farko. Mun same shi ne bayan shekara 17 ba haihuwa. Sannan bayan mun same shi kuma aka jarabce shi da wannan ciwon da ka gani.
Bayan na ji haka na kasa danne zuciyata idanuna suka cika da kwalla. Na ja mutumin zuwa cikin ofishina na ce da shi wannan matar taka wace iri ce wadda bayan shekara 17 na rashin haihuwa kuma take da irin wannan hakuri a kan manyan cututtukan da suka auka wa danta na farko? Zuciyarta ba sahara ba ce, tabbas jike take da imani. Kun san abin da ya ce? Ku saurara da kyau:
“Na zauna da ita tsawon shekara 19 a duk wadannan shekaru ban taba ganin ta tsallake wani dare ba tare da ta raya shi da tsayuwar dare ba, sai dai in da wani kwakwkwaran dalili. Ban taba samunta tana yi da wani ba, gulma ko karya ba. Koyaushe in zan bar gida ko zan shigo za ta bude mini kofa ta yi mini addu’a kuma ta karbe ni cikin karama. Kuma a cikin dukkan al’amuranta tana kai matuka wajen nuna kulawa, kauna da kyautatawa.”
Mutumin ya karasa da cewa “Saboda kyawawan dabi’u da so da kaunar da take huldantana da su, ina jin kunya in daga kai in kalle ta.” Na ce da shi irin wannan mace ta cancanci haka daga gare ka.
Darussa daga labarin wannan baiwar Allah shi ne Allah Ya azurce ta da dukkan da’a guda biyu, da’a ga Mahallicci (Tsarki ya tabbata a gare Shi) da kuma da’a ga mijinta. Da yawan mata a wannan zamani sun fi yin zurfi a daya ne kawai, ko dai a samu tsananin da’a ga Allah amma kuma a wajen da’a ga miji rauni ya yi yawa, ko kuma da’a ga miji ta yi tsanani ta yadda har a mance da’a ga Allah a rika sabonSa don neman soyayyar mijin. Sannan wannan labari ya nuna mana cewa in ka yi riko da Allah riko na gaskiya, ka kuma jajirce cikin rikon, to ba wani abu na faruwa a duniya da zai faru ya girgiza ka ya ta da maka hankali ko ya sa ka shiga mawuyacin hali. Sannan Ya koyar da mu cewa kankan da kai ga Allah na saukaka wa mace kankan da kai ga maigidanta.
Labari na 2
- “Wata matar aure ce a kasar Larabawa, da man ta kasance mai yawan yin Sallah farkon lokacinta, da ta ji kiran Sallah, za ta bar ko me take yi ta amsa kiran Ubangijinta. Wata rana sai mijinta ya ce ta yi masa wani abinci, shi wannan abinci ya kasance yana da wahala da daukar lokaci, kuma ana nannade shi a cikin ganye ne kamar dai yadda ake yin dan-gauda. Ta kusa gama nadewa don ta dora a wuta ke nan sai mijinta ya kira ta a waya yana sanar da ita ya yi kusan kamo hanyar gida daga wajen aiki. Ita kuma ta ce masa ita ma ta kusa hadawa, kafin ya iso abincin ya dahu. Ya rage saura kwara biyu ke nan ta karasa nadewa, sai aka kira Sallah, ta tashi tana murna don amsa kiran Ubangijinta. Maigida ya dawo ya same ta cikin Sujuda ya ga kuma ba a dora abinci ba, da ya duba ya ga kwara biyu kawai ya rage ta dora tukunyar, a fusace ya hau ta da fadan cewa kwara biyun kawai da za ta karasa sannan ta dora shi ne ta ki, yanzu ga shi ya dawo yana jin yunwa kuma ko dora tukunyar ba ta yi ba, zuwa can ya lura ta dade a sujudarta, yana zuwa ya dago ta sai ya ga ashe rai ya yi halinsa… Allahu Akbar! ’Yan uwana! Wannan shi ne alfanun sanya da’a ga Allah a gaba kuma sama da komai na rayuwar duniya. Kun ga wannan baiwar Allah da ta biye wa son faranta ran mijinta sama da amsa kiran Allah da a gaban murhu za ta mutu, ta koma ga Allah a lokacin da take kin yin da’a na amsa kiran yin munajati cikin Sallah da Shi Madaukakin Sarki. Amma da yake ta sa da’a ga Allah a gaba sama da komai da kowa a rayuwarta, sai ga shi ta samu kyakykyawan karshe, ta mutu a lokacin da take mafi kusantar Ubangijinta Allah Madaukakin Sarki. Da fatan Allah Ya sa mu dace, mu saka ayyukan neman kusanci Allah da gyara addininmu sama da komai a rayuwarmu, kuma Allah Ya sa mu dace da kyakykyawan karshe, amin.
Sai mako na gaba insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.