✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin Jam’iyyar LP sun kwashi ‘yan kallo a gaban Peter Obi a kotu

Fada ya kaure tsakanin jagororin bangarorin Jam'iyyar LP a yayin zaman Kotun Sauraron Karar Zaben Shuaban Kasa.

Fada ya kaure tsakanin jagororin bangarorin Jam’iyyar LP a yayin zaman Kotun Sauraron Karar Zaben Shuaban Kasa.

Rikicin ya faro bayan shugaban bangaren jam’iyyar, Lamidi Apapa da magoya bayansa suka hallara a harabar kotun da ke sauraron karar da jam’iyyar da dan takararta na zaben shugaban kasa, Peter Obi suka shigar na kalubalantar nasarar Bola Tinubu na APC.

Lamidi Apapa, wanda ke rikicin shugabanci da shugaban jam’iyyar da aka dakatar, Julius Abure, ya yi kokarin zama a inda jami’an jam’iyyar ta LP ke zaune, amma kan ka ce kwabo aka fara cacar baka.

Wani daga cikin jami’an jam’iyyar ya ce wa Lamidi, “Kai kuma daga ina?” inda shi kuma ya kada baki ya ce, “Ba ka san ko na waye ba; to kai waye kai? Ji yadda kake magana.”

Ana cikin haka, Apapa ya daga murya, ya ce masa, “Tashi ka bar nan, nan ba wurin saman irinka ba ne.”

Daga baya sakataren kotun, Josephine Ekperobe, ta shiga tsakani ta kwantar da kurar.

Daga bisani da kotun ta kira shari’ar jam’iyyar ta LP, Peter Obi da Jagorar Mata ta jam’iyyar, Dudu Manoga, suka gabatar da kansu.

Amma Apapa ya mike zai gabatar da kansa, a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, amma alkalin da kotun, Mai Shari’a Haruna Tsammani, ya dakatar da shi.

Ganin haka, sai Abure, wanda ke zaune kusa da Peter Obi, ya ki mikewa ya gabatar da kansa.

A baya dai Lamidi Apapa ya lashi takobin janye karar da ke gaban kotun, bayan da Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Abure.

Amma dai jam’iyyar ta daukaka kara.

A zaman nan ranar Laraba lauyan LP da na Bola Tinubu da na APC da na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za su gabatar da bayanin yadda suka hade batutuwan da kotun za ta yi shari’a a kansu.