✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa ya fice daga APC

Dan Majalisar Dattawan bai samu ko kira'a daya ba a zaben dan takarar gwamna a APC

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP.

Sanata Abdullahi Yahaya daga Jihar Kebbi ya ce fice da jam’iyyar ne bayan ya fadi zaben takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC.

Dan Majalisar Dattawan bai samu ko kira’a daya ba a zaben, sakamakon da ya yi watsi da shi a matsayin wasan yara.

Kakainsa, Muhammad Jamil Gulma, ya sanar cewa, “Shugaban Masu Rinjaye a Majsaliar Dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi zai bar Abuja da misalin karfe 9 na safiyar Laraba.

“Zai je Karamar Hukumar Kamba ta Jihar Kebbi inda zai sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a hukumance domin sake neman sake komawa kan kujerarsa.