✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban kasar Kyrgyzstan ya yi murabus

Shugaban kasar Kyrgyzstan, Sooranbi Jeenbekov ya sauka daga kujerarsa bayan kwana 10 ana rikicin siyasa a kasar. A ranar Alhamis shugaban ya sanar da saukara…

Shugaban kasar Kyrgyzstan, Sooranbi Jeenbekov ya sauka daga kujerarsa bayan kwana 10 ana rikicin siyasa a kasar.

A ranar Alhamis shugaban ya sanar da saukara domin kawar da fada tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar neman ya sauka daga mukaminsa.

Tun ranar 4 ga watan Oktoba Kyrgiztan ta fada cikin rikici bayan ’yan adawa sun yi fatali da sakamakon zaben da ya nuna abokan Jeenbekov ne suka lashe zaben Majalisar Dokokin kasar.

Daga shugaban ya soke zaben bayan’yan adawa masu zanga-zangar sun kwace gine-ginen gwamnati.

Ya kuma sanar a makon jiya cewa zai yi murabus amma ya jinkirta da cewa sai an yi wani zabe.

A ranar Laraba, Jeenbekov ya amince da zabin majalisar na Sadyr Japarov, don ya zama firai minista.