✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Amurka mai jiran gado ya nada dan Najeriya mukamin ma’aji

Zababben Shugaban Amurka, Joe Biden, ya ba dan asalin Najeriya, Adewale Adeyemo, mukamin Mataimaki Ma’ajin kasar. Anan sa ran Adayemo zai yi aiki karkashin tsohon…

Zababben Shugaban Amurka, Joe Biden, ya ba dan asalin Najeriya, Adewale Adeyemo, mukamin Mataimaki Ma’ajin kasar.

Anan sa ran Adayemo zai yi aiki karkashin tsohon shugabar asusun kasar, Janet Yellen, wadda ake sa ran za ta kula da asusun Amurka.

An haifi Adeyemo a shekarar 1981, kuma daya ne daga cikin mutum uku da Shugaban Amurka mai jiran gado ya zaba don su jagoranci kula da tattalin arzikin kasar.

Ragowar mutane biyun su ne; Cecilia Rouse da Neera Tanden, wanda aka ayyana a matsayin Darakta a Ofishin Kula da Kasafin Kudi.

Shi ne shugaba kungiyar ci gaban ’yan kasar Indiya mazauna Amurka kuma tsohon mashawarci kan tsare-tsaren yakin neman zaben tsohon Shugaba Barack Obama da Hillary Clinton.

Rouse, masanin tattalin arzikin kasashen Afirka da Amurka ne daga Jami’ar Princeton.

An zabe shi ya jagoranci majalisar mashawarta kan al’amuran da suka shafi tattalin Arziki.

Adeyemo tsohon mashawarci ne kan tattalin arzikin duniya lokacin gwamnatin Obama kuma shugaban gidauniyar Obama.

A 2015 an nada Adeyemo Mataimakin Babban Mashawarci kan sha’anin tsaron tattalin arzikin duniya kuma Mataimakin Darakta na Majalisar Tattalin Arziki na kasa.

Ya zama darakta a ofishin ’yan Afirka mazauna Amurka a ofishin yakin neman zaben John Kerry, a 2004.