✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin fim ya fi min siyasa – Mai Kwashewa

Ya kuma ce ba shi da aniyar tsayawa takara

Abdulrahman Muhammad wanda aka fi sani da Abdul Amart Mai Kwashewa, ya ce duk da yadda yake yin uwa da makarbiya a yakin neman zaben ‘yan siyasa, sana’arsa ta fim ta fiye masa siyasar.

Ya kuma ce ba shi da wata aniyar tsayawa takara duk da irin gudunmawar da yake bayarwa a yakin zaben ’yan siyasar.

Matashin mai shirya fina-finan dai ya ba da gagarumar gudunmawa wajen yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

A wata tattaunawarsa da Aminiya, Mai Kwashewa ya ce duk abin da yake yi ba don ci gaban kansa ba ne.

Ya kuma yi fice a wajen rarraba tallafi da kuma taimako ga ‘yan fim wanda hakan ta sa wasu ke masa lakabi da “Sardaunan ’yan fim mai kwana Kyauta”.

“Burina shine in ga masana’antar Kannywood ta samu tagomashin da za’a rika shirya fina-finai a kai-a kai don mutane su samu sana’ar yi,” inji shi.

Abdul Amart, wanda ya kafa kungiyar YBN don yakin neman zaben Yahaya Bello a matsayin Shugaban Kasa, ya kuma ce duk abin yake yi don ci gaban masana’antar Kannywood ne, amma ba don ya tsaya zabe ba.

Bayan da Shugaba Buhari ya samu nasara, ya jagoranci ‘yan fim sun gana da shi da kuma mai dakinsa, Aisha Buhari a lokuta daban-daban.

A wata amsar tambayar da Aminiya ta yi masa kan ko zai karbi mukamin siyasa idan aka ba shi sai ya ce, sai ya ce zai karba saboda masalahar Kannywood.