✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin City za ta iya lashe Kofin Zakarun Turai?

A kakar bara a wasan kusa da karshe aka cire City a Gasar Zakarun Turai.

A makon jiya ne Kungiyar Manchester City ta lashe kofin Firimiya ta Ingila bayan Kungiyar Nottingham Forest ta doke Kungiyar Arsenal da ci daya mai ban haushi, kwallon da dan Najeriya Taiwo Awoniyi ya jefa a ragar Arsenal a gidanta.

Wannan nasarar ce ta ba Kungiyar Man City damar lashe gasar Firimiyar Ingila karo na shida, sannan shi ne kofi na 12 da Pep Guardiola a zamansa a kungiyar, sannan yana shirin lashe biyu; na kalubale da zai buga wasan karshe da Kungiyar Manchester United a ranar 3 ga Yuni a filin wasa na Wembley da na Zakarun Turai da za su buga da Kungiyar Inter Milan da za a buga a ranar 10 ga Yuni.

A wasa 35 da Man City ta buga a bana, ta samu nasara a 27, inda ta zura kwallo 92, sannan ta samu maki 85.

Haka kuma da wannan nasarar, Man City ta lashe kofin Firimiya na Ingila sau uku ke nan a jere, wanda a tarihin gasar kungiyoyi hudu ne kawai suka taba irin haka, sai yanzu kungiyar ta zama ta biyar.

Kungiyoyin su ne; Huddersfield Town (1924 zuwa 1926) da Arsenal (1933 zuwa 1935) da Liverpool (1982 zuwa 1984) da Manchester United (1999 zuwa 2001 da 2007 zuwa 2009).

Sai dai a kullum ana jifan kungiyar da magana daya; sun dade suna lashe Firimiya ta Ingila tun kafin zuwan Guardiola, yaushe za su lashe Gasar Zakarun Turai?

Masu sharhi a kan harkokin kwallon kafa suna cewa dama asali an kawo Guardiola ne domin lashe Gasar Zakarun Turai ba don Firimiya ba domin ko kafin zuwansa kungiyar ta lashe Firimiya ba daya ba ba biyu ba.

Da yake jawabi bayan lashe Gasar Firimiya ta bana, Pep Guardiola ya ce lashe Gasar Zakarun Turai ne kadai zai daga darajar kungiyar sama da yadda take a yanzu.

Ya ce, “Wannan kungiya da ’yan wasan da muke da su a yanzu masu kokari ne sosai, kuma kungiyar na tashe matuka.

Amma ni ma na amince cewa idan muna so mu nuna matukar bajinta, dole sai mun lashe Gasar Zakarun Turai kamar yadda mutane suke fada wanda hakan ne zai sa kungiyar ta shiga cikin sa’o’inta na duniya.”

“Za mu ci gaba da fafutikar lashe Gasar Firimiyar Ingila. A kakar badi da karfinmu za mu shiga domin ba za mu gajiya ba.

“Ko a kakar bara a wasan kusa da karshe aka cire mu a Gasar Zakarun Turai, sannan bana muka sake zage damtse, ga shi bana mun kai wasan karshe.

“Dukkan kungiya mai nagarta ba ta gajiya da neman nasara. Don haka muna neman kari ne.”

Wannan nasarori da kungiyar take samu ana alakanta su da magance matsalarsu ta kakar bara ta rashin nagartaccen dan wasan gaba, wanda suka samu bayan dauko Erling Haaland.

Aminiya ta ruwaito a farkon kakar bana, inda a wasan farko da Manchester City ta buga, ta doke Kungiyar West Ham da ci 2-0.

Sai dai abin da ya fi jan hankalin mutane shi ne yadda matashin dan wasan, Erling Haaland ya kasance shi ne ya zura kwallo biyun a wasan.

Magoya bayan kungiyar sun je kallon wasan ne da zullumi, ganin fitaccen dan wasan ya gaza a wasansa na farko, inda Kungiyar Liverpool ta doke Manchester City a wasan Kofin Community Shield, wanda hakan ya sa wasu suke tunanin ko an yi sayen tumun-dare ne.

Sai dai wannan lokaci ne dan wasan yake ta ’yar gala-gala da gololin kungiyoyin Firimiya, inda a bana ya zura kwallo 52 a wasa 49 da ya buga.

Daga cikin kwallayen da ya zura, akwai kwallo 36 da ya zura a Firimiya, sannan ya zura kwallo 12 a Gasar Zakarun Turai duk da cewa ba a kammala gasannin biyu ba.

Dama dan wasan da Mbappe ne ake tunanin za su maye gurbin Messi da Ronaldo nan da dan lokaci kadan ganin yadda suke jan zarensu a yanzu.

A kakar bara, dan wasan ya zura kwallo 62 a wasa 67 da ya buga a Kungiyar Dortmund ta kasar Jamus, wanda hakan ke nuna bajintarsa.

Matashin dan wasa ne da ya kware wajen jefa kwallo a raga, sannan kungiyar Man City a karkashin jagorancin Pep Guardiola tana nuna kwarewa wajen taka leda da nemo hanyoyin zura kwallaye, amma a lokuta da dama a barnatar.