✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar Maina: Kotu ta kira Magu da Malami su ba da shaida

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta gayyaci Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da tsohon shugaban rikon Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC), Ibrahim Magu, su…

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta gayyaci Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da tsohon shugaban rikon Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC), Ibrahim Magu, su bayyana a gabanta don ba da bahasi a shari’ar shugaban rusasshiyar kwamitin gyara fansho, Abdualrasheed Maina.

Kiran, wanda aka gabatar a ranar 8 ga Maris, 2021 na zuwa ne daga mai shari’a, Okon Abang.

Sauran wadana alkalin ya bukaci su bayyana domin bayar da shaida su ne Daraktan Bin Ka’idoji na Babban Bankin Najeriya (CBN); M. Mustapha na Bankin Zenith Plc; da kuma Ibrahim Kaigama na Cibiyar Nazarin Manufofin Kasa da Nazari, Jos.

Kotu ta bukace su da su bayyana don bayar da shaida a madadin Maina a ranar 9, 10 da 11 na Maris daga karfe 9 na safe zuwa azahar.

Wani mai shaida, Ngozika Ihuoma a ranar Alhamis ya fada wa kotu cewa EFCC a karkashin Magu ta barnata kadarori 222 da kwamitin Maina ya kwato wadanda kudinsu ya kai Naira tiriliyan 1.63.

Ya kuma bayyana cewa daya daga cikin kadarorin da ake magana a kansu shi ne gini mai lamba 42, Gana Street, Maitama Abuja.

Shaidan ya ce Babban Lauya Najeriya, Femi Falana, ne ya sayi ginin ta haramtacciyar hanya, yayin da ake ci gaba da shari’a a kai.

Tuni dai Falana ya musanta ikirarin.