✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saurayin da budurwarsa ta cinna wa wuta a Makurdi ya mutu

Wani saurayi da budurwarsa ta banka wa wuta a Binuwai ya ce ga garinku nan a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Makurdi, babban birnin…

Wani saurayi da budurwarsa ta banka wa wuta a Binuwai ya ce ga garinku nan a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai.

Saurayin, mai suna Chidinma Ikechukwu Omah, ya rasu ne da misalin karfe 10 na daren ranar Litinin sakamakon radadin konuwar da ke jikinsa.

A halin da ake ciki, dangin mamacin sun karbi gawar dan uwan nasu domin fara shirye-shiryen binne shi.

Aminiya ta ruwaito cewa wata budurwa mai shekara 18, ta cinna wa saurayin nata wuta ne a kan titin Zaki-Biam da ke Unguwar Wadata a Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai.

Jami’ar Hulda da Al’umma ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai, DSP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce budurwar ta yi amfani da man fetur ne wajen cinna wuta a dakin da saurayin nata ke ciki.

Anene ta ce a halin yanzu budurwar ta shiga hannu kuma za a ci gaba da gudanar da bincike domin gano dalilin wannan danyen aikin da ta aikata.

“Ba mu da masaniya a kan dalilinta na aikata hakan, amma za mu yi mata tambayoyi kuma ina da tabbacin ta shiga hannu don yanzu haka an kawo mana ita.”

Aminiya ta samu cewa, Esther ta yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 2.00 cikin duhun dare a ranar Litinin.

Kazalika, rahoton ya nuna cewa makwabta ne suka ankara da lamarin da ke faruwa yayin da suka jiyo kururuwar matashin yana neman a kawo masa dauki.

Makwabtan sun kai wa matashin dauki wanda kusan duk jikinsa ya kone inda suka garzaya da shi Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Makurdi.

Wannan shi ne karo na hudu cikin watanni uku ake samun wani ya bankawa kansa ko masoyinsa wuta a Jihar.