✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saurayi ya saya wa budurwa fili a duniyar wata

Wani dan kasar Pakistan ya saya wa budurwar da zai aura fili a duniyar wata mai fadin eka daya a matsayin kyautar daurin aure ga…

Wani dan kasar Pakistan ya saya wa budurwar da zai aura fili a duniyar wata mai fadin eka daya a matsayin kyautar daurin aure ga matar.

Mutumin mai suna Sohib Ahmad, mazaunin Rawalpindi da ke kasar Pakistan ya sayi filin ne a wata nahiya da ake kira da ‘Sea of Vapour’ a duniyar wata.

  1. Saurayi ya kashe wanda ya haska fuskar budurwarsa da fitila a Kano
  2. Yadda wata budurwa ta mutu a dakin saurayinta

Kudin filin ya kai Dala 45 kuma ya saya ne daga Hukumar Filayen Kasa da Kasa ta Duniyar Wata.

A tsarin hukumar kamar yadda ta wallafa a shafinta na Intanet, “A karkashin yarjejeniyar LSI an sahale wa mutane mallakar filaye a duniyar wata ga daidaikun mutane domin su samar da kudin da za a gudanar da hakan ma’adinai da kawo ci gaba duniyar wata da kuma albarkatun da ke cikinta.”

Yarjejeniyar ta ci gaba da cewa “Da zarar an damka wa wanda ya mallaki filin shaidarsa, ta mallakar filin yana damar da zai gudanar da duk abin da ya yi kudiri a kai ta kowace hanya, sai dai idan akwai wata doka ko wata gwamnati da ke sararin samaniyar, wacce mutanen cikinta suka zaba.”

Ahmad ya ce, ya yi koyi ne da jarumin Bollywood, Sushant Singh Rajput, wanda ya sayi filinsa a duniyar wata. A 2018 Sushant ya sayi fili a Nahiyar Mare Muscoviense da ke duniyar wata a wajen Hukumar Kula da Rajistar Filayen Sararin Samaniya.

Budurwar da aka saya wa filin mai suna Madiha, ta ce a lokacin da take fada wa kawayenta game da filin da mijinta ya saya mata abin ya girgizasu.

“Daga farko kowa tsammani yake abin wasa ne, sai da na nuna musu takardun shaidar filin kafinsuka yarda da abin da nake faxa,” Madiha ta shaida wa Samaa TV.

Ta kara da cewa wata daga cikin kawayenta ma tana so wanda zai aure ta ya saya mata fili a duniyar wata.