✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sau daya na ci abinci a kwana uku a hannun masu garkuwa – Sarkin Rubochi

Garin Rubochi da ke Karamar Hukumar Kuje a Babban Birnin Tarayya Abuja, yanki ne da ya shahara wajen noma a tsakanin ’ya’yan kabilar Gbagyi da…

Garin Rubochi da ke Karamar Hukumar Kuje a Babban Birnin Tarayya Abuja, yanki ne da ya shahara wajen noma a tsakanin ’ya’yan kabilar Gbagyi da ke sarautar garin da sauran al’umma. Sai dai matasalar masu garkuwa da mutane da yanzu ta fara bayyana a yankunan Abuja, ta jefa tsoro a zukatan mazauna yankin tun a lokacin da masu garkuwar suka sace Sarkinsu, Alhaji Ibrahim Muhammad Pada a daren Laraba, 27 ga jiya.

Tuni dai aka sako Sarkin kwana uku bayan sace shi, bayan an biya Naira miliyan shida da rabi, kamar yadda wata majiya a fadar ta bayyana wa Aminiya. Bayan sako shi, ya kwanta asibiti na kwana shida a Abuja, kafin daga bisani ya dawo gida.

A zantawarsa da Aminiya a ranar Lahadin da ta gabata, Sarkin ya ce ya gode wa Allah da Ya dawo da shi kasarsa lafiya. Ya ce ba ya fata irin halin da ya same shi a lokacin, ya auku a kan koda makiyinsa ne.

Ku nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.