✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Sullubawan Katsina ya rasu

Marigayin Kani me ga Sarkin Katsina na yanzu

Allah ya yi wa Sarkin Sullubawan Katsina, Hakimin Kaita, Alhaji Abdulkarim Kabir Usman, rasuwa.

Ya rasu da yammancin Juma’a, kuma tuni aka gudanar da jana’izarsa a Fadar Sarkin Katsina.

Alhaji Abdulkarim dai kane ne ga Sarkin Katsina na yanzu, kuma shi ne jagoran duk wani Basulluben da ke masarautar ta Katsina.

An bullo da sarauta ta Sarkin Sullubawan ce da nufin hada kan ’ya’yan sarautar ta Sullubawa, aka kuma ba marigayin da hakimcin garin Kaita.