✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Funakaye Kwairanga ya rasu

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Funakaye, Alhaji Abubakar Muhammad Kwairanga II rasuwa. Bayanai sun ce sarkin ya yi mutuwar fuju’a ne a gidansa…

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Funakaye, Alhaji Abubakar Muhammad Kwairanga II rasuwa.

Bayanai sun ce sarkin ya yi mutuwar fuju’a ne a gidansa da ke Bajoga a Karamar Hukumar Funakaye ta Jihar Gombe a ranar Laraba da dare.

Majiyoyi a Bajoga sun ko a ranar Laraba, sai da marigayi Kwairanga ya wuni a garin Gombe ya kuma koma gida lafiya, har ya kwanta ba tare da cewar yana fama da wata matsala ba.

Kwatsam sai aka wayi gari da labarin rasuwarsa da safiyar Alhamis, yana da shekara 68.

Da karfe 2 na rana za a yi  jana’izar sa a garin Bajoga.