✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Daura zai nada Amaechi sarautar ‘Dan Amanar Daura’

Za a yi bikin nadin ne ranar biyar ga watan Fabrairun 2022.

Masarautar Daura ta kammala shirye-shirye tsaf domin nada Ministan Sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi, sarautar ‘Dan Amanar Daura’.

Matukar ba a samu wani sauyin shirye-shirye ba daga bisani, Sarkin na Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, zai nada Ministan ne ranar Asabar, biyar ga watan Fabrairun 2022, a fadarsa.

Tuni dai aka fara aike wa manyan bakin da ake sa ran za su halarci bikin katin gayyata, kuma rahotanni sun ce tuni shirye-shirye suka kankama.

A lokuta da dama dai, Sarkin ya sha fada cewa masarautar ba ta taba samun ayyukan ci gaba irin lokacin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba, wanda dan asalin garin ne.

Daga cikin manyan ayyukan da garin ya samu dai har da Jami’ar Sufuri, wacce Minista Amaechi ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kai ta Daura.

Sarautar Dan Amana na nufin wani wanda aka amince da shi a waje, watakila kuma Sarkin ya yi amfani da kusancin Amaechin da Shugaba Buhari.

An dai nada Amaechi ne a matsayin Minista a shekarar 2015, sannan aka sake nada shi a 2019, kuma ana ganinsa a matsayin wani babban na hannun daman Shugaban.

Ko kafin nan, shi ne ya zama shugaban yakin neman zaben Buhari a 2015 da 2019.