✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Birtaniya: An sa ranar bikin nadin Sarki Charles III

Fadar Buckingham ta sanar da 6 ga watan Mayu 2023 domin bikin sanya wa Sarki Charles kambin mulki

Fadar Buckingham ta kasar Birtaniya ta sanar da 6 ga watan Mayu, 2023 a matsayin ranar bikin sanya wa Sarki Charles III kambin mulki.

Fadar ta sanar a ranar Talata cewa a yayin bikin sanya wa Charles III mai shekara 73 kambi za a gudanar da al’adun shekara 900 tare da dacewa da zamani.

Sanarwar da masautar ta fitar ta ce, “Bikin nadin zai yi dubi da mas’uliyyar sarkin a yanzu da kuma nan gaba, tare da gudanar da al’adu masu dadadden tarihi.”

Bikin zai gudana ne a Westminster Abbey da ke birnin London, inda a lokacin ita ma matarsa Camilla, mai shekara 75, za a sanya mata nata kambin.

Ranar bikin, 6 ga watan Mayu ta zo daidai da bikin cika shekara hudu na jikan sarkin, Archie, wanda dansa, Yarima Harry da matarsa Meghan, suka haifa.

Sanarwar na zuwa ne wata guda bayan rasuwar mahaifiyar Charles, Sarauniya Elizabeth II, wanda ya haifar da kintace game da lokacin bikin nadin magajinta.

Charles ya zama Sarkin Ingila ne nan take bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth a ranar 8 ga watan Satumba, 2022.

Tun daga lokacin ya zama shugaban kungiyar kasashe 14 rainon Ingila, ciki har da Australia, Kanada da New Zealand.

Sarauniya Elizabeth ta rasu ne a gidan sarauta na Balmoral da ke yankin Scotlanda bayan fama da rashin lafiya tana da shekara 96.

Ta zama sarauniya tana da shekara 25 kuma ta kansace a kan karagar mulki na tsawon shekara 70, ita ce sarauniya da ta fi dadewa a kan mulki a tarihin Birtaniya.

Bayan rasuwarta, dubban daruruwan mutane sun yi dafifi a kan tituna domin ganin yadda aka dauko gawarta, sannan suka yi ta bin dogon layi na tsawon kwana hudu domin yi wa gawarta bankwana.

Ana sa ranar matuane masu yawan gaske kamar haka za su halarci bikin nadin sarautar Charles III, wanda rabon da a yi a kasar Birtaniya tun a shekarar 1953 da aka nada mahaifiyarsa.