✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarautar Zazzau: El-Rufai ya tabbatar da karbar sunaye

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbata karbar sunayen mutanen da za ta fitar da sabon Sarkin Zazzau daga ciki. Gwamna Nasir El-Rufai ya sanar da cewa…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbata karbar sunayen mutanen da za ta fitar da sabon Sarkin Zazzau daga ciki.

Gwamna Nasir El-Rufai ya sanar da cewa masu zabar sarki na Masarautar Zazzau sun mika wa gwamnatin jihar sunayen masu neman zama Sarkin Zazzau.

“Kwamishina da ke kula da harkokin masarautu na nazari kan sunayen ’yan takara 11 da masu zabar sarki suka mika masa.

“Daga baya zan yi nazari kan shawarar da ya bayar sannan ina zabi sabon sarki idan Allah Ya yarda”, inji shi.

Tuni wasu rahotanni suka tabbatar da cewa masu zabar sarki sun gabatar wa gwamnan da sunaye uku daga cikin mutum 11 da suka fito takarar zama Sarkin Zazzau na 19.

A ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020 Allah Ya yi wa Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Shehu Idris rasuwa bayan ya shekara 45 a kan mulki.