✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sanin darajar auren mata masu ilimi ya sa zan auri gwarzuwar musabakar Al-Qur’ani’

Irin wadannan mata ya kamata malamai da attajirai su rika aure.

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa sanin darajar ilimi ya sa zai auri wata Hafizar Al-Qur’ani a ranar Juma’a ta jibi.

Daurawa ya kuma ja kunnen wadanda suke yada hotunan kwalliyar matashiyar da zai aura da su daina wannan mummunar dabi’a.

Shehin Malamin ya bayyana cewa, hoton da ake yadawa na amaryar tasa a dakin babarta ana mata kwalliya wasu suka dauka ba a sani ba wanda hakan bai kamata.

A cikin wani katin gayyata da ke yawo a kafofin sada zumunta, ya nuna cewa Sheikh Daurawa zai angwance da gwarzuwar shekara a musabakar Al-Qur’ani ta kasa da aka gudanar tun a watan Maris na bana.

Gwarzuwar shekarar Haulatu Aminu Ishaq ta wakilci Jihar Zamfara a gasar Alkur’ani da aka yi ta kasa kamar yadda malamin ya bayyana a wata tattaunawarsa da Freedom Radio.

Malamin ya kuma kara da cewa, cin amana ne matuka yada hoton kwalliyar amaryar tasa, kuma ita kanta ba ta ji dadin hakan ba, wanda hakan ya sa ranta ya dugunzuma matuka, ta yi kukan bakin cikin yadda hoton kwalliyar  ya yi yawo a soshiyal midiya.

“Wannan duk ya san ya sa ya je ya goge domin kuwa sun aikata fasadi,” a cewar Daurawa.

Har wa yau, ya kara da cewa, sanin darajar auren mata masu ilimi ya sa zai auri wannan hazika a bangaren Kur’ani.

A karshe, Malamin ya kara da cewa da ma haka ya kamata attajirai da malamai su rika yi wajen aure ‘yan matan da suka nuna bajinta a bangaren addini ba a “shadaicin banza ba.”