✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samun ’yancin Najeriya: Me Buhari zai ce bayan shekara 61

Nasara koma baya da kalubalen da Najeriya ke fuskanta bayan shekara 61.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi kan cika shekara 61 da samun ’yancin kasar.

Buhari zai yi jawabin ne da misalin karfe 7 na safe, ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba, 2021, wanda shi ne ranar bikin zagayowar samun ’yancin kasar.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya sanar da hakan, yana mai kira ga tashoshin rediyo da talabijin na Gwamnatin Tarayya su kamo tare da yada jawabin shugaban kasar kai tsaye.

– Nasara ko koma baya?

Ana sa ran jawabin shugaban kasar na zagayowar ranar samun ’yancin Najeriya zai tabo bangarorin da dama, musamman nasarori da kalubalen da kasar ke fuskanta, watakila har da albishir.

  1. Tattalin arziki

Tattalin arzikin Najeriya dai na cikin wani yanayi, ganin yadda kasar ke cikin tsaka mai wuya, musamman yadda alkaluman hukumomin kudade na duniya suka sa ta a cikin jerin manyan masu cin bashi na duniya.

Akwai kuma faduwar darajar Naira da na farashin danyen mai a kasuwar duniya, baya ga tasirin annobar COVID-19 da har yanzu kasashe ba su gama murmurewa daga gare shi ba.

A bayan nan ne dai Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dauki matakin hana ’yan canji Dala, ya kuma mayar da harkar canji zuwa hannun bankunan kasuwanci, a yunkurinsa na kare darajar Naira; Sai dai har yanzu da alama haka ba ta cim ma ruwa ba.

A ranar bikin zagayowar ranar samun ’yancin Najeriya na bana kuma CBN zai kaddamar da tsarin kudin intanet na Najeriya, wato E-Naira.

A shekarar ce kuma aka fara aiwatar da Dokar Man Fetur (PIA), wadda ake sa ran hakan zai bunkasa tattalin arziki a bangaren man fetur.

Sai dai kuma farashin danyen mai ya yi kasa a kasuwar duniya, a cikin gida kuma farashin gas din girki sai tashi yake ta yi, a yayin da ’yan kasar ke kokawa game da tsadar man fetur.

Baya ga haka, karin farashin wutar lantarki ya haifar da ce-ce-ku-ce, a inda akasarin ’yan Najeriya ke kokawa game da rashin ingatacciyar wutar, da kuma matsin rayuwa, musamman bayan bullar cutar COVID-19.

  1. ’Yan bindiga

Akwai kuma matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa da wadansu ke dangantawa da yawaitar matsalolin tsaro a sassan kasar.

Zagayowar ranar samun ’yancin Najeriya na kuma zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke daukar matakan murkushe ayyukan ’yan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso Gabas da Arewa da Tsakiya.

’Yan bindiga sun raba mutane da dama da garuruwansu, sun kona gidaje, sun yi wa mata fyade, sun yi garkuwa da mutane da dama — ciki har da dalibai masu yawa a makarantu daban-daban, baya ga manyan mutane da sauran al’umma — suka kashe wasu, wasu kuma suka biya makudan kudade a matsayin fansa.

A jihohin Zamfara da Katsina da Sakkwato da Kaduna an rufe layukan sadarwar tare da haramta wasu harkoki domin ba wa sojoji damar yi wa ’yan bindiga luguden wuta, musamman a Jihar Zamfara.

Gwamnatocin jihohin na ikirarin samun nasara a sakamakon daukar matakan, duk da cewa ba a rasa samun hare-hare a kan kauyuka da jami’an tsaro.

  1. Ta’addanci

A yankin Arewa maso Gabas kuma an kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, wanda a sakamakon haka mayakan kungiyar da iyalansu sama da 5,000 suka mika wuya.

Kazalika, an kashe shugaban kungiyar ISWAP, Abu Mus’ab Al-Barnawi, wanda bayan mutuwar Shekau ya mamaye kungiyar Boko Haram.

Duk da haka ana ci gaba da tababa tsakanin hukumomi da al’umma kan kokarin dawo da tubabbun mayakan ISWAP da Boko Haram da iyalansu cikin jama’a da zama.

Kafin nan, mayakan Boko Haram sun kai munanan hare-hare kan sansanonin soji a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji da dama, baya ga kisan gilla da suka yi wa mutane da dama, ciki har da wasu manoma suka yi wa yankan rago da dai sauransu.

A halin yanzu kuma gwamnatin Najeriya na ta yin odar jiragen yaki domin yakar ta’addanci, kuma wasu daga cikin jiragen sun iso kasar.

  1. Mutuwar sojoji

A baya-bayan nan jiragen soji sun kashe mutane da dama a jihar Yobe a bisa kuskure, a yayin yakar kungiyoyin ’yan ta’adda.

Kazalika a cikin shekarar nan, jiragen soji da dama sun yi hatsari, ciki har da wanda ya yi sanadiyyar mutuwar tsohon Babban Hafson Sojin Kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahihu da ’yan tawagarsa.

Wani hari da aka kai a makarantar horas da kananan hafsan sojin Najeriya (NDA) inda suka kashe wani mai mukamin Manjo suka sace wani ya haifar da ce-ce-ku-ce kan yanayin tsaro hatta a cibiyoyin tsaron kasar.

  1. ’Yan a-ware

A yankin Kudu maso Gabas kuma akwai rikicin kungiyar IPOB mai neman ballewa daga Najeriya, inda ta tsananta kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati da kashe mutane da babu ruwansu, baya ga tursasa musu zaman gida.

A shekarar nan dai an kama shugaban kungiyar Nnamdi Kanu, wanda a baya ya tsere, sannan kotu ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi.

Shi ma mai fafutikar neman ballewa don kafa kasar Yarabawa zalla ta Oduduwa, Sunday Igboho ya shiga hannu har an kai shi kotu.

  1. Yajin aiki

Gwamnatin na fama da matsaloli kuma da ma’aikata, inda likitoci ke yajijn aiki, makamancin haka kuma na kasa tana dabo a tsakanin gwamnatin da malaman jami’a.

  1. Rikice-rikice

Rikicin kabilanci da na manoma da makiyaya shi ma daya ne daga cikin matsalolin da suka dade suna ci wa Najeriya tuwo a kwarya.