✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Salon yakin Boko Haram bayan sojoji sun kassara ta

Kungiyar Boko Haram ta fara amfani da sabon salon amfani da kananan yara a matsayin mayaka a yankin Tabkin Chadi. Rundunar Tsaron Hadin Gwiwar kasashen…

Kungiyar Boko Haram ta fara amfani da sabon salon amfani da kananan yara a matsayin mayaka a yankin Tabkin Chadi.

Rundunar Tsaron Hadin Gwiwar kasashen yankin (MNJTF) a wata sanarwa ta ce kungiyar ta koma jefa kananan yaran cikin hadari ne saboda daruruwan mayakanta suke ficewa suna tuba.

“Sun koma amfani da kananan yara ne saboda yara sun fi saukin a juya musu tunani domin manya a yankin sun riga sun gane yaudarar kungiyar”.

Sanawar da kakakin rundunar, Kanar Timothy Antiga ya fitar ranar Alhamis ta kara da cewa sakamakon binciken sirin da MNJTF ta yi ya dace da abun da ‘yan kasa da kungiyoyi masu kishi suka gano.

Janar Antiga ya ce Boko Haram ta tabbatar da cewa tana amfani da yara a matsayin mayaka kamar yadda tana tuna wasu kananan yara dauke da bindigoi a wani bidiyo da kungiyar ta fitar da Babbar Sallah.

“A baya Boko Haram ta yi ta sace dalibai mata, suna bautar da su da aurar da su ga mayakansu, da kashe-kashen fararen hula”, inji sanarwar.

Ya kara da kira ga iyaye da hukumomi da sarakunan yankin da su rika lura tare da sanar da jami’an tsaro game da duk wani yunkuri na shigar da ‘ya’yansu cikin kungiyar.

Antiga ya shawarci matasa da su yi hattara da romom baka da kungiyar ke musu na samun iko da dukiya ko imani da suke ta yi, sakamakon mika wuyan da mayakansu suka yi.

Karon farko ke nan da MNJTF ke tabbatar da cewa kuniygar na amfani da kananan yara a matsayin mayaka, duk da cewa wasu rahotannin Asususn Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya jima da tabbatar da hakan a cikin wani rahoto.

Ana kuma zargin sojojin da amfani da kanana yara a cikin civilian JTF, sai dai har yanzu sojojin ba su amsa zargin ba.