✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Salman Rushie Zai Iya Rasa Idonsa Bayan Harin Da Aka Kai Masa  

Ba kamar yadda ake yadawa a shafukan sada zumunta da muhawara, fitaccen marubucin nan Salman Rushdie wanda aka kai wa hari a Amurka yana samun…

Ba kamar yadda ake yadawa a shafukan sada zumunta da muhawara, fitaccen marubucin nan Salman Rushdie wanda aka kai wa hari a Amurka yana samun sauki daga raunukan da aka ji masa.

Wata hira da aka babban jami’in ’yan sandan birnin New York na kasar Amurka ya ce marubucin na samun sauki daga raunukan da ya samu sai dai zai iya rasa idonsa daya.

Rushdie wanda aka garzaya da shi asibiti rai-kwakwai, mutu-kwakwai, har ma an cire masa injin din da ke taimaka masa yana numfashi a karshen makon da ya wuce, inji dansa, Zafar Ruhdie.

“Sai dai ana ci gaba da yi masa maganin raunukan da ya samu wadanda suka hada da sukar wuka da aka yi masa a wuya har sau uku, da wani sukar har sau hudu a cikinsa.

“An kuma yi masa wani sukan a kusa da idanunsa na dama da kirji, da wani yanka a cinyarsa ta dama.

“Sai dai ana fargabar zai rasa iya idanun na sa na dama a sakamakon sukar,” in ji kami’in.

Wani matashi mai suna Hadi Matar ne ya yi kukan kura ya far wa marubucin a daidai lokacin da yake shirin gabatar da wani jawabi da wata cibiya ta gayyace shi a New York.

Rushdie mai shekara 75 shi ya rubuta wani littafi mai suna Ayoyin Shaidan wanda a ciki ya yi batanci ga Manzo Allah [SAW] a shekarar 1989 wanda ya fusata al’ummar Musulmi, kuma aka ba da fatawar kisa a kansa.

Tun daga lokacin ya shiga buya a kasar Ingila, daga baya ya koma da zama kasar Amurka.