✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallar Layya: Farashin man gyada ya yi tashin gwauron zabo a Kano

Galibi farashinsa kan tashi lokutan bukukuwan Sallah

A duk lokacin da Azumi ko bukukuwan Sallah ko na Kirsimeti suka karato, wani sashe ko duka kayayyakin masarufi kan yi tashin gauron zabo a kasuwanni, daidai da abin da aka fi bukata a wannan lokacin.

Malaman addini da masana, har ma da al’umma sun sha kiraye-kiraye da jan hankali kan illar hakan a addinnance da kuma ga tattalin arzikin kasar.

Sai dai bisa ga dukkan alamu wa’azin na shiga ne ta kunnen ‘yan kasuwar na dama ya fice ta hagu, domin kuwa har yanzu ba abin da ya sauya daga wannan dabi’a ta su.

‘Yan kasuwar dai sun sha kare kansu kan wannan zargin da dalilai irin su tashin sinadaran samar da wutar lantarki ko farshin gas ko na man dizel, wanda injinan sarrafawa ko dauko kayayyakin ke aiki da su, ko ma a wasu lokutan kudin harajin da gwamnati ta sanya musu.

A bana ma kamar kowacce shekara, gabatowar Sallar Layya ya sanya tuni man gyada da na kuli-kuli da ma farin mai, suka yi tashin gwauron zabo, inda suka ninka kudin man fetur da ake kukan tsadarsa a fadin kasar nan kusan sau uku.

Yanzu dai litar man gyada kadai ta kai Naira 950, a daidai lokacin da farashin man fetur din ba wuce lita Naira 180 zuwa 200 ba.

Wannan ma, a cewar wasu daga cikin ‘yan kasuwar da muka zanta da su, farashin na somin tabi ne, domin su da kansu na kukan zai dara haka idan an zo gab da Sallar da aka fi bukata domin suyar naman Layya.

Ita ma shinkafar dafawa da danya su aka fi sarrafawa a abincin bikin Sallar, na ta hawa da sauka a kasuwar, wato wani satin su yi sama, wani su sakko kadan, amma dai sun haura farashin Sallah karama.

Mun zagaya kasuwannin Galadima Road da Singa da ke Kano, inda mutane ke dafifin sayen man da shinkafa in da muka lura babu masu hada-hadar saye da wuri, wanda a baya a daidai wannan lokacin al’umma kan yi dafifin don tanadarsu tun kafin farashinsu ya yi hawan da ba za su iya sayen isassu ba.

Dalilin tashin farashin man

A kasuwar Galadima Road da ke Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano, wacce ita ce babbar kasuwar hada-hadar mai da kifi, mun tattauna da wani mai siyar da mai da ya nemi mu sakaya sunansa kan farshin man a yanzu.

Ya ce yanzu haka jarkar farin mai Naira dubu 32 suke sayar da ita, yayin da duron suke sayar da shi a kan Naira dubu 180.

Ya ce “Kasancewar makonni biyu da suka gabata an samu karin N7,000 kan ainihin farashinsa na baya, shi ya sa aka samu wannan karin farashin mai yawa”.

Kazalika ya ce farin mai na kasar waje  ya kai N29,000 sai kwanturola da jarkarsa ta kai N31,000.

Da muka tambaye shi dalilin samun wannan hawan farashin sai ya ce, “Hakan na da nasaba da karin kudin haraji da tashin farashin mai da sinadarin dizel da injinan sarrafa man ke aiki da su, don mu ma haka manyan ‘yan kasuwan da muke karbo man a gurinsu suke fada mana.

“Da idonki kin gani babu kwastomomi a kasuwar nan. A da sai mu samun ribar N7,000 a tashi daya, yanzu idan ka samu 300 to ka gode wa Allah, saboda ga tsada ga babu masu saye.

Duron Mai
Duron Mai

Dan kasuwar ya ce sati hudu da suka gabata, sukan sami mutane 100 su shigo kasuwar sayan man, amma bayan samun karin yanzu ba a samun fiye da 30.

“Matsalar nan ta samo asali ne tun a shekarar 2017, misali a baya wajen shekarar 2010 zuwa 2016 man bai fi Naira 5,000 ba jarka, yanzu kuma shekara bakwai kacal daga wancan lokaci ya koma fiye da N30,000.

“Kin kuma san albashin ma’aikaci ba motsawa yake ba a Jihar, to talaka ba shi da wannan kudin ya zai yi? Kin ga dole ba za a samu ciniki ba. Ga shi sakamakon haka ‘yan kasuwa da dama daga cikinmu ma sun daina siyar da man,” in ji shi.