✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah: DSS ta gargadi al’umma bayan kama bindigogi a Kano

Muna fatan musulmi za su yi shagulgulan sallah lafiya.

Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS, sun cafke wasu ’yan bindiga da manyan bindigogi biyu wadanda suka boye a cikin buhun doya a Jihar Kano.

An kama ababen zargin biyu ne yayin da suka ratso ta Kano da zummar isar da sakon bindigogin zuwa wata jiha a Arewacin Najeriya da ake shirin kaiwa hari a shirye-shirye mika wa sabuwar gwamnati mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Mai magana da yawun ’yan sandan na sirri, Peter Afunanya ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Abuja, yana mai cewa an samu mutanen biyu da bindigogi biyu kirar AK-47 da kuma kwanson alburasai na bindigogin.

Afunanya ya ce an samu wani babur kirar boxer da kuma wani buhun doya inda ababen zargin suka boye bindigogin.

Babban jami’an na DSS ya kirayi masu wuraren shakatawa a fadi jihar da su yi taka-tsan-tsan musamman masu otel-otel da su inganta tsaro a daidai wannan lokaci na shagulgulan sallah.

“Muna kira ga al’umma da su zama masu lura a koyaushe tare da gaggauta sanar da duk wani motsi da ba su aminta da shi ba zuwa ga hukumar tsaro mafi kusa.

“Da wannan kuma muna taya al’ummar musulmi murna kuma da fatan za a yi shagulagulan sallah lafiya.”