✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah: An ninka kudin tikitin jirgin sama

Ana biyan N122,000 daga Legas zuwa Sakkwato a a Arik Air

Kasa da mako guda kafin Karamar Sallah, kamfanonin jiragen sama sun ninka kudin tikiti, kamar yadda binciken Aminiya ya gano. 

Aljihun masu shirin tafiya hutun Sallah a jirgin sama zai koka, inda wasu za su biya abin da ya kai N122,000, ko su bi mota a tituna da ke fama da rashin kyau da kuma ’yan bindiga.

Matafiyan da wannan tsadar ta fi shafa su ne masu zuwa Arewacin Najeriya daga Legas — zuwa Abuja da Kano da Katsina da Sakkwato da Yola da sauransu, inda kudin tafiya falle-daya yake kaiwa har N122,000.

Duk da haka tikitin jirgi zuwa Kudanci bai wuci N50,000, kamar daga Legas zuwa Abuja da Legas zuwa Fatakwal da kuma Legas zuwa Uyo.

A watan Fabrairu ne dai aka kara kudin tikitin jirgi falan-daya zuwa N50,00, wanda kamfanonin jirgi suka dora laifin kan tsadar man jirgi, lamarin da ya fusata ’yan Najeriya.

Daga baya Gwamnatin Tarayya ta shiga cikin lamarin ta hannun hukumominta ta bukaci a soke karin kudin man, duk da haka wasu kamfanonin ba su bi umarnin ba.

A yanzu da Karamar Sallah ta karato kuma, matafiya a lokacin za su biya karin kashi 30 zuwa 80 cikin 100 a kan kudin jirgi daga yankin Kudanci zuwa Arewacin Najeriya.

Yanayin tsadar

Karin zai shafi matafiya ne daga ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu zuwa 2 ga watan Mayu, ranar da ake sa ran hutun Karamar Sallah da gwamnati za ta bayar zai kare.

Yanzu dai ma’aikata da ’yan kasuwa da sauran Musulumi na shirye-shiryen Sallah, amma da alama  matafiyan da ba su sun sayi tikitin jirgi tun da farko ba, musamman zuwa wuraren da jirage ba su fiye zuwa ba, su wannan tsadar za ta fi shafa.

Aminiya ta gano cewa an ninka kudin jirgin Max Air daga Abuja zuwa Kano zuwa N100,000 daga N50,000, tafiyar da ba ta wuci minti 40 ba.

An kara kudin Air Peace daga Legas zuwa Abuja, daga N50,000 ya koma N60,000 zuwa N70,000.

Legas zuwa Kano a Azman Air zai yana kamawa daga N63,878 zuwa 94,835, daga ranar Alhamis zuwa Lahadi.

Ba mu da zabi —Matafiya

Wani dan kasauwa a Legas, Abdullahi AbdulAzeez, ya shaida wa wakilinmu cewa ya samu tikin N60,000 zuwa Kano a Max Air saboda tun da wuri ya saya, duk da cewa farashin ya fi asalin kudin tikitin na N50,000.

“Zan je Sallah Kaduna ranar Alhamis, amma jirgin Kano zan bi, amma ba don rashin kyan hanya ba da Abuja zan sauka.

“Abokina ma’aikacin Max Air ne ya saya min tikitin, cewa yana kara kudi. Idan na sauka a Kano, sai in karasa Kaduna, maimakon bin hanyar Abuja zuwa Kaduna inda ake yawan sace mutane.”

Ya zargi kamfanonin jirage da amfani da karatowar lokacin Sallah da kuma rashin tsaro wajen tsawwala farashi.

Wani Bakano mazaunin Legas da ke shirin zuwa gida ranar Laraba ya koka kan tsadar tikicin.

Ya ce ba don wani abu ba da mota zai bi, saboda yana da kaya da yawa, wanda hakan zai ci karin kashe kudi ta jirgi.

“Amma rashin tsaro ba zai bari ba, mutane da yawa ba za su yi gangancin bin mota ba,” inji shi.

Dan dama-dama

Amma Aminiya ta gano kudin jirgi daga Abuja zuwa Maiduguri a Azman na nan a yadda yake N50,000, la’alla saboda yawan matafiya.

Abuja zuwa Gombe da Lega zuwa Kano a jirgin ma bai karu ba daga N63,878.

Tikiti mafi tsada shi ne na Legas zuwa Sakkwato a Arik Air, wanda ke farawa daga N108,214 zuwa N122,196. Arik na zuwa Sakkwato daga Legas sau uku a mako.

Abuja zuwa Sakkwato a Max Air kuma kudinsa N100,000, daga ranar Talata.

Arik Air ya kara kudin Legas zuwa Benin daga N50,000 zuwa 86,978, sannan Legas zuwa Yola ya koma N86,500 daga N70,000.

Zuwa ranar Litinin da muka bincika, ba a kara kudin Legas zuwa Ilori daga N50,000 ba, amma an kara na Abuja zuwa Ilori zuwa N70, 000.

Ya fi na kasar waje tsada

Fasinjojin jiragen sama na kokawa cewa zirga-zirgar jirage a cikin gida a Najeriya ya fi na fi na kasashen Turai tsada, duk da cewa man jirgi ya fi tsada a Turai.

Kamfanonin jiragen sama a Najeriya dai sun dora laifin karin farashin a kan tsadar man jirgi da suka ce yanzu suna sayen lita a kan N500.

Amma wata majiya ta shaida mana cewa zirga-zirgar jiragen sama na da araha matuka a kasashen Turai da kuma Birtaniya.

Binciken wakilinmu ya nuna tafiyar minti 55 a jirgin Ryan Air daga Dublin a kasar Ireland zuwa Manchester a Birtaniya bai wuce Yuro 14 ne (kimanin N6,220 a kan canji N450).

Kamfanonin jirgi

Kamfanonin jirage sun dora laifin karin da suka yi a kan yanayin kasuwa da tsadar kudadaden da suke kashewa na gudanar da aiki.

Wani mamba a Kungiyar Kamfanonin Jiragen Sama ta Najeriya (AON), Barista Barrister Shehu Wada, ya ce, “Yanzu da kyar kamfanonin jiragen sama ke gudanar da harkokinsu saboda tsadar abubuwa.”

Ya ce duk da umarnin gwamanti, har yanzu ba a rage kudin man jirgi ba.

Game da arahar kudin jirgi a Turai, ya ce watakila gwamnatocin kasashen suna ba da tallafi ga kamfanonin jirage.

Shi kuma wani mai kamfanin jirage da aka tambaya cewa ya yi, “Ya zan sayi mai da tsada kuma in zo in ci gaba da karbar tsohon farashi? Rashin lissafi ke nan.

Mun nemi kakakin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), Sam Adurogboye, wanda ya ce gwamnati ta dade da cire hannunta a bangaren sufurin jiragen sama, yanzu yanakin kasuwa ne ke yi alkalanci a harkar.

“Idan kamfani ya kara kudi, ka je wurin wani, idan ba su samu kwastomomi ba dole su rage,” inji shi.

Wani mai sharhin sufurin jiragen sama, Farfesa Anthony Kila, ya bayyana cewa karin ba mugunta ba ce, yanayin tattalin arziki ne ya kawo hakan.

Ya ce an samu karin ne kawai a wuraren da babu fasinjoji sosai, a sauran wurare kamar Abuja zuwa Legas yana nan yadda yake.

“Idan gwamanti na son taimakawa, sai ta rage harajin da take karba daga kamfanonin,” saboda duk tikitin da aka saya tana karbar haraji a kai.