✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sako Zakzaky: ‘Ba ma son ya sake dawowa cikinmu’

Ba mu ji dadi ba da aka ce an sako malamin.

A watan jiya ne Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayar da umarnin a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zarge-zargen da ake yi musu.

Tun a shekarar 2015 ce aka kama malamin da matara bayan arangamar da mabiyansa suka yi da sojoji a Zariya.

SAURARI: Abin da Ya Faru A Afghanistan Zai Yiwu A Najeriya?

Bayan sakinsa, hankali ya koma kan yadda zai dawo ya ci gaba da harkokinsa a gidansa da aka rushe da kuma makarantarsa.

Ba ma bukatar da dawowarsa —Mutanen Gyallesu

Sai dai da Aminiya ta ziyarci Unguwar Gyallesu, inda gidan malamin yake, don zantawa da mazauna unguwar kan yadda suka ji, bayan sun samu labarin sako malamin, da dama daga cikinsu su nuna damuwarsu kan yiwuwar dawowar malamin unguwarsu.

Wani dattijo mai kimanin shekara 70 wanda kuma ya kwashe sama da shekara 30 yana zaune a Unguwar Gyallesu da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun hadu da ukuba da kaskanci wanda ba ya da bambanci da zaman bauta a lokacin da malamin yake zaune tare da su.

Ya ce hakan ya sa ba su ji dadi ba da aka ce an sako malamin.

Ya ce ai abin da ya faru a fili yake, don haka duk da su addininsu ya hana tashin hankali kuma ya umarce su da su yi wa gwamnati biyaya, “Amma a wannan lokacin idan har an ce zai sake dawowa Gyallesu da zama to za mu shirya,” inji shi.

Ya kara da cewa ba za su yarda da irin abin da aka yi musu a baya ba.

Da yake nasa tsokaci, Malam Sidi Inuwa da ke zaune a Layin Wali a Unguwar Gyallesu, a kan ko za su so su ci gaba da makwabtaka da Malam Zazzaky cewa ya yi, “To kamar yadda ka bukaci ra’ayina shi ne jin wannan maganar taka har ka sa na tuna abin da ya faru a baya.

A lokacin da Malam Zakzaky ya bakunce mu, mun yi murna da zuwansa a matsayinsa na bako kafin daga baya lamari ya canja.”

Malam Sidi Inuwa ya kara da cewa, “Mun dandana kudarmu domin a wancan lokacin kamar ba mu da gwamnati idan wata matsala ta hada ka da mabiyansa babu inda za ka kai kara sai dai wajen Allah, har Allah Ya kawo karshen lamarin muna raye sannan a ce wai za a sake dawowa da shi, ai gara in bar unguwar in tafi wata unguwar in karasa rayuwata a can.

“Don haka, ba ma fatar haka ya sake faruwa a wannan lokaci da muke raye kai ko bayan ranmu. Saboda mu ba ma goyon bayan a sake dawo da shi wannan unguwar,” inji shi.

Shehu Yunus (ba sunansa na asali ba) da ke sayar da shayi a Layin Makama, Gyallesu, ya ce ba ya da wata damuwa a kan sake dawowar Malam Ibrahim Zazzaky da kuma zama a Unguwar Gyallesu domin shi harkarsa yake yi kuma bai taba samun matsala da wani mai goyon bayansa ba.

Ba ma karatu ko taro a gidan Malam — IMN

Aminiya ta tuntubi Kungiyar IMN, wadda malamin yake jagoranta domin jin ta bakinta kan yadda take shirin ci gaba da gudanar da karatuttuka ga mabiyansa.

Malam Abdulhamid Bello wakilin Kungiyar IMN a Zariya ya ce dama can ba sa karatu a Gyallesu domin a can gidan malaminsu yake, sai dai mutane masu kai masa ziyara su je can amma ba wai a shirya karatu ba.

Ya kara da cewa amma karatunsu yawanci a cikin unguwanni suke yi tun kafin waki’ar da aka yi har zuwa yanzu kuma ba su daina yin karattutukansu ba.

“Hakikanin gaskiya ko da Malam yake unguwar ba a yin wani karatu a can Gyllesu.

Gidan Malam ne yake can sai dai a kawo wa Malam ziyara a gidansa.

Sai dai a can Husainiyya da ke a Titin Sakkwato mutane suke haduwa a yi karatu “Kuma ko a yanzu idan Malam ya dawo sai dai a ce ya je ya zauna a gidansa amma ba wai dama don ana yin karatu a wurin ba ne.

Ba ma wani karatu ko gudanar da abubuwa a Gyallesu baki daya sai dai zaman Malam a matsayin gidansa.

“Ban da wannan kuma wurare a cikin gari ko Sabon Gari ko Tudun Jukun ko Tudun Wada da kuma nan cikin Zariya har Samaru da wurare daban-daban da muke gudanar da abubuwanmu har yanzu ana yin karatuttukanmu ba wata matsala.

“Tun Malam yana tsare har yanzu ballantana a ce dama an rufe bari a dawo da su. Babu abin da ya canja,”inji shi.

Waiwaye

A shekarar 2015 ce aka kama Malam Zakzaky da matarsa Zeenat bayan arangamar sojoji da mabiya Zakzaky lokacin da suka samu sabani wadda ta yi sanadiyar mutuwar daruruwar mabiyan malamin.

An kama malamin ne bisa zargin kisa da yin gangami ba tare da izini ba da kuma ta da zaune-tsaye.

Bayan kama shi, mabiyansa sun yi ta gudanar da zanga-zanga kan a sako shi, inda a nan ma aka sha yin arangama tsakaninsu da jami’an tsaro, aka raunata da dama, aka kashe wadansu jami’an tsaro da mabiya malamin.

A watan jiya ne wata Babbar Kotun Jihar Kaduna, ta wanke malamin daga dukkan zarge-zargen da ake yi masa shi da matarsa Zeenat.