✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sabon Sarkin Zazzau ya kai ziyara Masarautar Kano

Duk abin da ya shafi Masarautar Kano, mu ma ya shafe mu.

A Larabar da ta gabata ne Sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya kai ziyarar ban girma fadar Sarki Kano, inda ya yi wa Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero mubaya’a tare da jaddada kudirinsa na karfafa alakar shekaru aru-aru da ke tsakanin Masarautun biyu.

Sarki Bamalli ya ce tawagarsa ta kai wa Masarautar Kano ziyara ne domin kara dankon zumuncin da ke tssakanin Masarautun biyu tun zamanin Mujaddadi Shehu Usman dan Fodio.

Basaraken ya lura cewa Masarautar Kano da ta Zazzau sun dade tare tamkar ’yan uwan juna inda ya ke fatan su ci gaba dorewa a kan hakan.

“Muna sane da dadaddiyar kyakkyawar dangartakar da ke tsakanin Marigayi Sarki Kano, Alhaji Ado Bayero da kuma Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.”

Yayin da aka yi zaman fada a Masarautar Kano tare da Sarki Bamalli
Sarkin Bamalli tare da Sarki Aminu Bayero

“Duk abin da ya shafi Masarautar Kano, mu ma ya shafe mu, ba don muna makwataka ba sai don mun kasance ’yan uwan juna.”

“Ina son na sanar da cewa duk gidajen masarautar Zazzau dangi daya ne, kuma a cikin wannan tawaga akwai wakilcin daga kowane daya daga cikin gidajen.”

“Wannan shi ya nuna cewa kasha 95 cikin 100 na masu mukamai da Hakimai a shirye suke wajen ganin Masarautar ta samu ci gaba,”a cewar Sarki Bamalli.

Shi ma a nasa jawabin, Sarki Aminu Bayero ya taya Ambasada Bamalli murna kan nadin da aka yi masa a matsayin Sarkin Zazzau na goma sha tara.

%d bloggers like this: