✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya shiga ofis

Sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Abubakar Lawal, ya shiga ofis a ranar Juma'a

Sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Abubakar Lawal, ya kama aiki a Hedikwatar rundar jihar da ke Bompai.

An nada Lawal ne a ranar Laraba bayan tsohon Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sama’ila Shuaibu Dikko, ya yi ritaya daga aiki.

Dikko ya yi ritaya daga aikin dan sanda ne bayan ya cika shekara 60 da haihuwa a ranar 27 ga watan Yuli, 2022, kuma shi ne  na 42 a jerin Kwamishinonin ’Yan Sanda da aka yi a jihar Kano.

Kafin yanzu Lawal, wanda shi ne Kwamishinan ’Yan Sandan JIhar na 42, ya kasance Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Inugu.