✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon Birni: ’Yan bindiga sun kara kashe mutane bayan ziyarar Tambuwal

Sa'o'i kadan bayan Gwamna Jihar Sakkwato ya kai ziyarar ta'aziyyar mutanen da ’yan bindiga suka kashe aka kai sabon harin

’Yan bindiga sun hallaka mutum uku a kuayen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jibar Sakkwato.

Maharan sun kai farmakin ne a yayin da ake Sallar Isha ranar Alhamis, sa’o’i kadan ziyarar ta’aziyyar da Gwamnan Jihar Sakkawto, Aminu Waziri Tambuwal, ya kai wa iyalan mutanen da ’yan bindiga suka yi wa kisan gilla a yankin.

“Da dare ana Sallah suka shigo suka rika luguden wuta kan mai tsautsayi har suka kashe mutum uku suka jikkata wasu da dama da a yanzu ake ba su kulawa a asibiti,” inji wani mazaunin kauyen.

Gwamna Tambuwal ya kai ziyarar ce domin jajanta wa al’ummar Sabon Birni kan rasuwar matafiya 42 da ’yan bindiga suka yi kona kurmus a cikin motarsu a hanyar Sabon Birni zuwa Isa a ranar Litinin.

A lokacin ziyarar gwamnan ya ba wa iyalan mamatan tallafin N250,000.
A lokacin hada wannan rahoton, wakilinmu ya nemi samun karin bayani daga kakakin ’yan sanda na Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar amma hakan bai samu ba.