✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabbin abubuwan da ke faruwa a yakin Rasha da Ukraine

Netflix, TikTok, Master Card da Visa sun rufe harkokinsu a Rasha; Gwamnati ta kayyade sayen kayan abinci

Ma’aikatar tsaro ta Ukraine ta ce mayakan sa-kai 20,000 daga kasashen duniya za su taimaka wa kasar wajen yakar Rasha; Amma Shugaban Rasha, Vladimir Puti, ya ce kasarsa ce da nasara, ko ta sulhu, ko ta yaki.

A yayin da kasashen ke ci gaba da gwabza fada a tsakaninsu, kafar sada zumunta ta TikTok da kuma Netflix mai yada fina-finai ta intanet sun dakatar da harkokinsu a Rasha.

Su ma manyan kamfanonin katin cirar kudi na Master Card, Visa da sauransu sun rufe harkokinsu a Rasha, inda gwamnatin kasar ta kayyade sayen kayan abinci a halin yanzu.

Ga jerin sabbin abubuwan da suka faru:

– Ruwan bama-bamai –

Sojojin Rasha sun tsananta luguden bama-bamai yi a sassan kasar Ukraine inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum akalla miliyan 1.5 sun tsere a cikin kwana 10 da aka fara yakin.

Ta ce rabon da mutane masu wannan yawa su fice da wata kasa a cikin kwana 10 tun a lokacin Yakin Duniya II.

– Fararen hula sun makale a Mariupol –

Yunkurin kwashe fararen hula daga birnin Mariupol ya sake gagara kan zargin saba yarjejeniyar tsagaita wuta.

Mazauna birnin suna fama da rashin ruwan sha da wutar lantarki; Amma ma’aikatar tsaron Rasha ta ce za ta bari a gudanar da ayyukan jinkai a wasu sassan Ukraine.

– Musayar wuta –

Sojojin Ukaine sun ce an ci gaba da kazamin fada tsakaninsu da dakarun Rasha a kusa da birnin Mykilayiv da ke Kudancin kasar.

Birnin Mykilayiv na kan hanyar zuwa babbar tashar jiragen ruwan Ukraine da ke  Odessa.

– An ragargaza Chernihiv –

An kashe fararen hula da dama a Chernihiv da ke Arewacin Ukarine.

Wadanda ke da ransu kuma sun koma zama a cikin baraguzan gini da kangaye.

– An lalata filin jirgi –

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi zargin cewa makamai masu linzami da Rasha ta harba sun lalata filin jirgin Vinnytsia da ke tsakiyar kasarsa.

– Rasha ta kayyade sayen kayan abinci –

Rasha ta kayyade wa masu kantuna sayar da muhimman kayan abinci a yunkurinta na yakar labarin da ke cewa takunkumin da Kasashen Yamma suka kakaba mata za ta kara muni.

– An tsare dubban masu zanga-zanga –

Jami’an tsaron Rasha sun tsare wasu dubbun mutane da suka fito zanga-zangar kyamar yakar Ukrain da kasar ke yi.

Daga fara yankin zuwa yanzu, mutanen da aka tsare kan gudanar da zanga-zanga sun haurwa 11,000.

– Duk yadda ta juya mu ne a sama —Putin –

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce kasarsa za ta cim ma manufar da ta sa gaba a Ukraine, “ko ta sulhu ko ta yaki”.

– Poland za ta ba Ukriane jiragen yaki –

Amurka ta amince kasar Poland ta tura wa Ukraine jiragen yaki, abin da Putin ya yi gargadi cewa na iya tsoma kasashen kungiyar tsaro ta NATO a yakin da babu ruwansu.

– Takunkumin danyen mai –

Sakataren Amurka, Antony Blinken ya ce Kasashen Yamma na duba yiwuwar kaurace wa danyen man da Rasha ke samarwa.

Sai dai ko a yanzu farashin gangar danyen mai samfurin Brent na Amurka ya doshi Dala $140, wanda shi ne mafi tsada.

– Rufe katin cirar kudi –

Manyan kamfanonin cirar kudi na Visa, Mastercard da kuma American Express sun rufe harkokinsu a Rasha.

Amma bankunan Rasha sun ce za su koma amfani da UnionPay na kasar China.

– Ficewar kwararru –

Manyan kamfanonin kwararru na KPMG da PwC sun rufe harkokinsu a Rasha, wanda ke nufin mutum 8,200 za su rasa ayyukansu. 

Shi ma kamfanin kwararru na Deloitte na nazari kan yiwuwar zama ko ficewa daga kasar.

– Fargabar nukiliya –

Faransa ta ce za ta tura wa Ukraine kwayoyin magani na iodine da sauran magunguna domin kare mutane daga illar tuturin nukiliya.

– Mayakan sa-kai –

Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya ce mayakan sa-kai 20,000 daga kasashen duniya, yawancinsu daga kasashen Turai, za su hada kai da kasarsa domin yi wa Rasha taron dangi.

– Ficewar kamfanonin fasaha –

Netflix ya dakatar da harkokinsa a Rasha, sannan TikTok ya toshe duk sakonnin bidiyo daga can.

– Kafafe yada labarai sun daina aiki –

Kafafen yada labarai na kasashen duniya irinsu BBC, CBC, ARD, ZDF, Bloomberg News, CNN, CBS, RAI da kuma EFE sun daina aiki a Rasha bayan ta yi dokar da ta tanadi hukunci dauri ga masu fitar da rahoton yakin.