✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rufe kafofin yada labarai da Gwamnatin Zamfara ta yi ya saba doka’

Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su guji kawo cikas ga ci gaban da aka samu na dimokuradiyya.

Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai ta Najeriya (NBC), ta ce matakin rufe wasu kafofin yada labarai da Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi a ranar Asabar ya saba wa doka.

Shugaban NBC, Balarabe Shehu Ilelah, ya ce sun sanar da Gwamnatin Zamfara karara irin saba wa dokar da aka yi.

“Mun fada wa gwamnati ta bai wa al’ummar jihar hakuri,” a cewarsa cikin wata sanarwa.

“Sannan mun shawarci jami’an tsaro da su share umarnin da aka ba su na hana ma’aikatan kafofin da abin ya shafa yin aikinsu na halali.”

A ranar Lahadi Kwamashinan Yada Labarai na Zamfara, Ibrahim Dosara ya bayyana cewa an rufe kafofin watsa labaran ne saboda sun yada taron jam’iyyar adawa ta PDP duk da cewa Gwamnatin Jihar ta hana tarukan siyasa saboda dalilai na tsaro.

Ya ce Majalisar Tsaro ta Zamfara ce ta amince tare da ba da umarnin rufe kafofin labaran da suka kunshi Rediyo Najeriya da Pride FM Gusau da NTA Gusau da Gamji Talabijin da Vision FM da Al Umma TV.

NBC ta kara da cewa “muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su guji kawo cikas ga ci gaban da aka samu na dimokuradiyya a Najeriya.”