✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya yi watsi da tayi mai tsoka na wata kungiya a Saudiyya

Bayern Munich da Atletico Madrid sun soma zawarcin Ronaldo.

Dan wasa gaba na Manchester United dan kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya yi watsi da wani gwaggwaban tayi da wata kungiyar kwallon kafa a kasar Saudiya ta yi masa.

Bayanai sun ce kungiyar ta yi wa Ronaldo tayin kudi har Yuro miliyan 300 domin ya buga mata wasanni na tsawon kaka biyu.

Sai dai jita-jitar kasuwar musayar yan wasa a bana na cewa, bayan sanar da aniyarsa ta yin watsi da tayin ne kungiyoyin Bayern Munich da Atletico Madrid suka bayyana sha’awar raba shi da Ingila.

Sai dai rahotanni na cewa, Bayern Munich za ta sayi dan wasan mai shekara 37 da zarar ta cefanar da dan wasan gabanta na kasar Poland, Robert Lewandowski da ke shirin tafiya Barcelona.

Barcelona ta shirya tsaf domin kara kaimi wajen sayen Lewandowski mai shekara 33 kan Yuro miliyan 50.

Har yanzu dai Ronaldo bai kai ga hadewa da tawagar Manchester United a ragadin tinkarar kaka mai zuwa da suke a Asiya da Australiai ba, saboda abin da mai horar da ‘yan wasan kungiyar ya kira dalilai na kashin kansa.

Ronaldo ba na sayarwa ba ne —Ten Hag

Sabon kocin na Manchester United, Erik ten Hag ya bayyana karara cewa tauraron dan wasansa na gaba Cristiano Ronaldo ba na siyarwa bane a kakar wasa ta bana, duk da cewa dan wasan na son rabuwa da Old Trafford.

Kawo yanzu an shafe fiye da makonni uku ana tofa albarkacin baki kan matakin Ronaldo na bayyana aniyarsa ta rabuwa da Manchester United, saboda yana da muradin taka leda a gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa, to amma ga dukkanin alamu kungiyar ba ta damu da hakan ba, inda ta sanya shi cikin shirin tawagar ta a kakar wasa ta 2022/23.

Yayin tsokaci kan makomar Ronaldo, Erik Ten Hag ya ce ko shakka babu an fadi abubuwa da dama, da kuma rubuce-rubuce game da Ronaldo, wanda baya cikin tawagar United da ta ziyarci kasar Thailand da kuma Australia ba, kuma hakan ta faru ne saboda wasu batutuwa na sirri, amma fa abinda ya sani shi ne cewar dan wasan na cikin tsarinsa a bana.

Sabon kocin na Manchester United ya kuma tabbatar da cewa mai tsaron baya, Harry Maguire ne zai ci gaba da zama kyaftin din kungiyar duk da cewa dan wasan na Ingila na shan caccaka da izgili daga magoya baya da dama.

Dalilin da Ronaldo ke son barin United

Tun bayan bude kasuwar musayar ’yan wasan ce Ronaldo ya bukaci United da ta kyale shi ya kara gaba muddin har ta samu tayin da ya dace da shi.

Wannan dai na zuwa ne bayan United ta kare a matsayi na shida a teburin Firimiyar Ingila, don haka ta rasa tikitin shiga gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

Ronaldo wanda ya koma Old Trafford daga Juventus a bazarar da ta wuce, shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a kakar wasan da ta wuce – kuma na uku a gasar Firimiyar Ingila – ana kallon kakar wasannin da ta shude a matsayin babbar koma baya a gareshi.

Hakan na nufin Ronaldo, wanda ke da sauran kwantiragin shekara daya da United, zai fuskanci doka wasannin gasar Europa a karon farko, wanda shi kuma ya ke ganin kwarewarsa ba ta wannan gasa ba ce sai ta Zakarun Turai.