✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya ja wa Coca-Cola asarar Dala biliyan 4

Hannun jarin Coca-Cola ya fadi warwas bayan Ronaldo ya nuna kyama ga lemun kamfanin.

Shahararren dan kwallon kafar kasar Portugal da kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo, ya ja wa kamfanin Coca-Cola tafka asarar fiye da Dala biliyan hudu.

Darajarar hannun jarin kamfanin Coca-Cola ya fadi warwas a fadin duniya, sakamakon kyamar da dan wasan ya nuna kan dangogin kayan shaye-shayen kamar giya da sauran lemuka masu dauke da sunadarin benzoic acid wanda a Turance ake kira ‘Carbonated Drinks’.

A yayin taron manema labarai gabanin wasan da Portugal za ta fafata da Hungary a gasar EURO 2020 ne Ronaldo ya nuna kyamarsa ga irin wadannan kayan lemu, wadanda a ganinsa suna yaki da ingatttaciyar lafiyar dan Adam.

Gabanin fara tattaunawa da manema labaran a ranar Litinin ne Ronaldo ya sauke wasu kwalaben lemu na Coca-Cola da aka jera saman teburin da ya zauna.

Ganin an ajiye kwalaben lemon na Coca-Cola a gaban teburin da yake zaune ke da wuya, dan wasan ya yi maza ya sa hannu ya kawar da su.

Daga nan ya dauko wata gorar ruwa yana mai nuna alamar cewa idan mutum yana son zama cikin koshin lafiya, to ya mayar da ruwa abin shansa a kodayaushe, madadin ire-iren wadancan lemuka.

Tun a ranar Litinin din dan wasan ya shiga kanun labarai saboda yadda ya gwale kwalaben lemukan Coca-Cola guda biyu; Cikin mintuna kadan abin ya karade shafukan sada zumunta.

Cristiano Ronaldo ya shahara wajen tsantsenin kula da lafiyarsa, wanda haka ya  sa ya dade a kan ganiyarsa kuma har yanzu hasken tauraruwarsa a kwallon kafa ba ta disashe ba, duk kuwa da cewa ya kai shekara 36 a duniya.

A baya dai Ronaldo ya taba nuna kyamarsa ga lemukan kwalba inda ya ce ya tsani ganin dansa ma yana shan lemukan.

Jaridar Marca, mai rubuta labaran wasanni ta kasar Spain, ta ruwaito cewa darajar hannun jarin Coca-Cola ya fadi da biliyoyin daloli idan aka kwatanta kafin da kuma bayan matakin da Ronaldon ya dauka.

Marca ta ci gaba da cewa darajar kamfanin ya fadi daga Dala biliyan 242 zuwa 238 wanda shi ne kashi 1.6% a kasuwar hannayen jari.

A yayin wasan da aka fafata ranar Talata, Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu a ragar Hungary inda aka tashi wasa Portugal din na da ci uku yayin da Hungary take nema.