✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Zangon Kataf: An bukaci a hukunta Zamani Lekwot

Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeria ta nemi Gwamnatin Tarayya da ta sake duba hukuncin da aka yanke wa Zamani Lekwot da sauran shugabannin…

Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeria ta nemi Gwamnatin Tarayya da ta sake duba hukuncin da aka yanke wa Zamani Lekwot da sauran shugabannin Kudancin Kaduna dangane da rawar da suka taka a rikicin Zangon Kataf a shekarar 1992.

A cewar majalisar rashin yanke musu hukuncin kisa kamar yadda kwamitin binciken da aka kafa a wancan lokaci ya nemi a yi shi ya sa ake ci gaba da rikici a yankin.

Sakataren Majalisar a Jihar Kaduna Injiniya Abdulrahman ne ya bayyana matsayin majalisar akan Rikicin Kudancin Kaduna a zantawarsa da manema labarai a ranar Alhamis.

“Akwai matsaloli da ke faruwa a wannan yankin wanda an rasa rayuka da dukiyoyi kuma tun shekarar 1981 ake wannan rikici.

“A shekarar 1987, mun ga abun da ya faru a Zangon Kataf yadda aka karkashe Musulmi aka kone musu dukiyoyi.

“Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin bincike ta kuma binciko wadanda ke da laifi, a kuma zartar masu da hukuncin kisa amma gwamnatin wancan lokaci ta yafe musu.

“Yafiya da aka yi musu ita ce ta janyo mana matsalar da muke ciki a yanzu domin Allah Ya ce. Duk wanda ya kashe idan ya san za’a kashe shi ba zai yi ba”, inji shi.